logo

HAUSA

Zambia Da MDD Sun Yabawa Shirin Sin Na Samar Da Karin Alluran Rigakafin COVID-19 Ga Duniya

2021-08-08 16:30:16 CRI

Gwamnatin kasar Zambia da jami’an MDD sun yaba wa shirin gwamnatin kasar Sin na samar da karin alluran rigakafin COVID-19 ga duniya.

A baya-bayan nan ne kasar Sin ta sanar da cewa, za ta yi kokarin samar da alluran rigakafin COVID-19 biliyan 2 ga duniya a bana, tare da bayar da dalar Amurka miliyan 100 ga shirin COVAX, wanda zai mayar da hankali kacokan wajen rabon rigakafi ga kasashe masu tasowa.

Da yake tsokaci game da wannan sanarwa, Kennedy Malama, babban sakataren kula da harkokin fasaha a ma’aikatar lafiya ta kasar Zambia, ya ce wannan kokari ne mai kyau da zai tabbatar da samar da rigakafin ga kasashe kan kudi kalilan.

Ya kara da cewa, matakin zai kai ga tabbatar da rabon rigakafin cikin daidaito ga kasashe masu tsananin bukata.

A nasa bangaren, Nathan Bakyaita, wakilin hukumar lafiya ta duniya WHO a Zambia, ya ce kokarin na kasar Sin ya cancanci yabo, saboda annobar COVID-19 ta yi mummunan tasiri kan tattalin arzikin galibin kasashe masu tasowa.

Ya ce an kafa shirin COVAX ne da nufin tabbatar da daidaito wajen rabon rigakafin, yana mai cewa, kokarin na kasar Sin zai taimaka gaya wajen tabbatar da hakan. (Fa’iza Mustapha)

Fa’iza Mustapha