logo

HAUSA

Amurka ba ta da hurumin sukar kasar Sin ba tare da dalili ba

2021-07-23 19:23:49 CRI

Amurka ba ta da hurumin sukar kasar Sin ba tare da dalili ba_fororder_中美2

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Zhao Lijian, ya ce Amurka ba ta da hurumin baiwa kasar Sin horo, ko sukar kasar ba tare da sahihan dalilai ba, ballantana yin barazanar hukunta Sin ta duk wata hanya.

Zhao ya yi wannan tsokaci ne, a yayin taron manema labarai na rana-rana da aka saba gudanarwa na yau Juma’a, lokacin da yake tsokaci game da tambayar da aka yi masa, don gane da shirin ziyarar da mataimakiyar sakataren wajen Amurka Wendy Sherman za ta yi a Tianjin nan ba da jimawa ba.  (Saminu)

Saminu