logo

HAUSA

Sama da yara miliyan 4 sun kamu da COVID-19 a Amurka

2021-07-22 11:05:26 CMG

Sama da yara miliyan 4 sun kamu da COVID-19 a Amurka_fororder_ibrahim-2

Wani sabon rahoto da cibiyar kula da lafiyar kananan yara ta Amurka (AAP) da kungiyar asibitoci masu kula da kananan yara suka wallafa, ya nuna cewa, sama da kananan yara miliyan 4 a kasar Amurka ne,suka kamu da cutar COVID-19, tun lokacin da annobar ta bulla a kasar zuwa yanzu.

A cewar rahoton, ya zuwa ranar 15 ga watan Yuli, kimanin kananan yara miliyan 4.09 ne cutar ta harba. Sai dai bayan an samu rahoton raguwar masu kamuwa da cutar a cikin ‘yan watanni, yawan masu kamuwa da cutar ya karu a watan Yuli.

Rahoton ya kara da cewa, sama da kananan yara 23,500 ne aka ba da rahoton sun kamu da cutar a makon karshe na ranar 15 ga watan Yuli. Kananan yara na wakiltar kaso 14.2 cikin 100 na dukkan masu kamuwa da cutar a kasar ta Amurka.

A cewar rahoton, yaran da aka kwantar a asibiti, sun kai kaso 1.3 zuwa 3.6 cikin 100 na yawan wadanda aka kwantar a asibiti sanadiyar cutar, yayin da cutar ta halaka kaso 0 zuwa 0.26 cikin 100 na dukkan wadanda cutar ta yi ajalinsu.(Ibrahim)

Ibrahim