logo

HAUSA

Sudan ta bukaci a cimma matsaya tsakanin bangarorin dake rikici da juna a yankin Tigray na Habasha

2021-07-05 10:01:49 CRI

Sudan ta bukaci a cimma matsaya tsakanin bangarorin dake rikici da juna a yankin Tigray na Habasha_fororder_11

A jiya Lahadi kasar Sudan ta bukaci dukkan bangarorin dake fada da juna a yankin Tigray na kasar Habasha da su dakatar da fadan da suke gwabzawa kana su zauna a teburin tattaunawar sulhu.

A wani babban taron tattaunawar da ya gudana a Khartoum, babban birnin kasar Sudan, an bayyana matukar damuwa game da halin da ake ciki a Habasha inda ake fargabar cewa rikicin zai iya haifar da mummunan tasiri game da makomar zaman lafiyar shiyyar, musamman makwabtan kasashe, majalisar mulkin kasar Sudan ce ta bayana hakan cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta kara da cewa, makomar kasar Habasha ya dogare ne kan ‘yan kasar Habashan kuma idan aka yi la’akari da yanayin dangantakar kasar da makwabtan kasashe gami da moriyarsu, Sudan ba ta da wani zabi da ya rage face tsayawa tsayin daka wajen yin aiki da dukkan bangarorin da abin ya shafa a rikicin Habashan domin kokarin cimma matsaya wanda zai kawo hadin kan kasar Habasha.

Tashin hankalin ya barke ne a farkon watan Nuwambar bara a shiyyar arewacin yankin Tigray na kasar Habasha tsakanin dakarun tsaron kwatar ‘yancin yankin Tigray, wato TPLF, masu fafutukar karbe ikon shiyyar, da dakarun tsaron gwamnatin kasar Habasha.

Sabon rikicin ya sake barkewa a yankin Tigray a kan iyakar yankin da kasar Sudan bayan ‘yan tawayen sun yi nasarar sake karbe iko da birnin Mekelle a makon jiya wanda ke zama helkwatar shiyyar.(Ahmad)