logo

HAUSA

Sojojin Somaliya sun kashe mayakan al-Shabab a kalla 7 a tsakiyar kasar

2021-05-10 10:30:04 CRI

Sojojin Somaliya sun kashe mayakan al-Shabab a kalla 7 a tsakiyar kasar_fororder_210510-dakarun gwamnatin Somaliya

Rundunar sojojin gwamnatin kasar Somaliya (SNA), ta sanar cewa ta kashe a kalla mayakan al-Shabab 7 bayan wani farmaki da dakarun na  SNA suka kaddamar a kusa da gundumar Mahas dake shiyyar Hiran a tsakiyar kasar Somaliya.

Mohamud Hassan Ibrahim, kwamandan rundunar SNA na shiyyar, ya bayyanawa gidan radiyon gwamnatin kasar dake Mogadishu cewa, sun kuma jikkata wasu mayakan na al-Shabab kimanin 17, kana sojojin gwamnatin sun kone wata tankar yaki mallakin al-Shabab a lokacin artabun.

Ibrahim ya ce, manufar kaddamar da farmakin shi ne domin kwato yankunan da har yanzu suke karkashin ikon mayakan al-Shabab da kuma tabbatar da ganin ana gudanar da zirga-zirga a manyan titunan motan kasar.

Har yanzu babu wani martani daga bangaren mayakan game da ikirarin da dakarun sojojin na SNA suka yi dangane da farmakin sojojin a shiyyar tsakiyar kasar. (Ahmad Fagam)