logo

HAUSA

Mike Pompeo zai kammala aikinsa na ministan harkokin waje

2021-01-20 16:34:18 CRI

Mike Pompeo zai kammala aikinsa na ministan harkokin waje_fororder_微信图片_20210120163348

A cikin kwanaki 10 da wani abu da suka gabata, Mike Pompeo ya aiwatar da jerin matakai, wato soke takunkumin hana jami’an Amurka tuntubar yankin Taiwan na kasar Sin, da sake shigar da Cuba cikin jerin sunayen kasashe masu goyon bayan ta’addanci, da kara kakabawa kasar Iran takunkumi.

Ban da wannan kuma, ya wallafa sakonni fiye da 60 a shafinsa na Twitter a cikin kwanaki 3, inda yake cika baki kan abubuwan da ya yi wai ya yi nasara a matakan da ya dauka kan kasar Sin, da ma takalar manufofi da jam’iyyar JKS da kasar Sin suka dauka.

Duk wadannan abubuwan da ya yi na rashin imani, ya bayyana rauninsa na rike wannan mukami mai muhimmanci. Matakan siyasar da Mike Pompeo ya dauka za su kawo babbar illa ga fadin duniya, saboda yadda yake kare moriyarsa fiye da muradun kasar.

Mike Pompeo ya nunawa duniya ainihin fuskar gwamnatin Amurka na girman kai da rashin sahihanci da babakare, kana duniya ta kara fahimtar ma’anar tsarin dimokuradiyya da ‘yancin dan-Adam mai salon Amurka. Amma, wa’adinsa ya kare, duk matakin da ya dauka ba zai yi wani amfani ba. (Amina Xu)