logo

HAUSA

Kasar Sin ta ci gaba da zama a kan gaba a fannin cinikayyar hajoji ta yanar gizo

2021-01-20 11:52:09 CRI

Kasar Sin ta ci gaba da zama a kan gaba a fannin cinikayyar hajoji ta yanar gizo_fororder_src=http___5b0988e595225.cdn.sohucs.com_images_20180907_d21e3391ea1c44338589a403dd85f131.jpeg&refer=http___5b0988e595225.cdn.sohucs

Alkaluman da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta fitar jiya Talata na nuna cewa, yawan hajojin da kasar ta sayar ta kafar intanet, ya karu da kaso 14.8 cikin 100 bisa makamancin lokaci na bara, adadin da ya kai kudin Sin RMB Yuan triliyan 9.8, kwatankwacin dalar Amurka triliyan 1.5 a shekarar 2020.

Wannan na nuna cewa, kasar Sin ta kasance babbar kasuwar sayar da hajoji ta Intanet a duniya cikin shekaru 8 a jere. Yawan hajojin da kasar ta sayar ta intanet, ya kai kaso 24.9 na yawan hajojin da kasar ta sayar a shekarar da ta gabata.

A shekarar 2020, cinikayyar Intanet ta kafar bidiyo kai tsaye ya samu karbuwa, inda aka gudanar da harkokin cinikayya sama da miliyan 20 kai tsaye ta kafar bidiyo.

Alkaluman ma’aikatar sun kara nuna cewa, yawan kayayyakin da kasar ta shigo da su daga ketare, shi ma ya karu da kaso 8.2 cikin dari kan na bara, inda darajarsa ta kai Yuan triliyan 1.57.(Ibrahim)

Ibrahim Yaya