logo

HAUSA

Cinikin Sin da kasashen waje ta intanet zai kai dala triliyan 3 a 2022

2021-01-03 16:07:51 CRI

Cinikin Sin da kasashen waje ta intanet zai kai dala triliyan 3 a 2022_fororder_1208-1

An yi hasashen hada hadar kasuwancin kasar Sin da ketare ta intanet zai iya kaiwa yuan triliyan 20.5, kwatankwacin dala triliyan 3.15 a shekarar 2022, kamar yadda wani rahoto ya bayyana.

A shekarun baya bayan nan, an samu bunkasuwar kasuwanci ta intanet tsakanin kasar Sin da kasashen waje, inda fannonin kanana da matsakaitan kamfanonin kasuwanci ta intanet suke ci gaba da samun bunkasuwa a duk shekara da kusan kashi 30 bisa 100, kamar yadda rahoton hukumar kiyaye mallakar fasahar kira ta kasar Sin ya bayyana.

Kasuwancin na zamani wanda ya tsallaka kan iyakokin kasashe ya taka gagarumar rawa wajen tabbatar da safarar hajoji bisa daukar matakan yaki da annobar COVID-19, kana ya taimakawa kasa da kasa a yayin da ake fama da annobar, a cewar rahoton.

Yayin da fannin ke ci gaba da samun nasarori, rahoton ya bukaci kasa da kasa su dauki matakan kare hakkin mallakar fasahohin kira domin tabbatar da gudanarwar fannin hada hadar kasuwancin ta intanet a kasashen duniya.(Ahmad)