logo

HAUSA

Gwamnatin Sudan ta nanata kudirinta na kare rayukan fararen hula a yankin Darfur da tashin hankali ya barke

2021-01-20 11:12:09 CRI

Gwamnatin Sudan ta sake nanata kudirinta na kare rayukan fararen hula da samar da tsaro a yankin Darfur, inda tashin hankalin kabilancin da ya barke a yankin ya yi sanadin rayukan gwamman mutane.

Wata sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar, ta bayyana takaici kan yanayin tsaron da ake ciki a wasu sassan yankunan kudancin da yammacin Darfur. Ma’aikatar ta kuma sake nanata nauyin dake wuyan gwamnati, na tabbatar da tsaro da kare rayukan fararen hula a dukkan sassan kasar, inda yanzu haka, gwamnati da abokan hulda dake kokarin tabbatar da zaman lafiya, suke kara kaimi wajen sauke wannan nauyi.

Wasu alkaluma da ba na hukuma ba, sun nuna cewa, fadan kabilancin da ake ci gaba da gwabzawa a yankunan yammaci da kudancin Darfur, ya yi sanadin rayukan mutane 184, kana sama da mutane 200 kuma sun jikkata.(Ibrahim)

Ibrahim Yaya