logo

HAUSA

Yawan wadanda suka mutu sanadiyar harin ’yan bindiga a yammacin Darfur na Sudan ya kai 83

2021-01-18 09:46:48 CRI

Rahotanni daga jihar yammacin Darfur ta kasar Sudan na cewa, yawan wadanda suka mutu sanadiyar harin da ’yan bindiga suka kaddamar a El Geneina, babban birnin jihar, ya kai 83, kana wasu 160 kuma sun jikkata.

Wata sanarwar da majalisar rikon kwaryar kasar Sudan ta fitar na nuna cewa, hukumar tsaron kasar ta yanke shawarar tura karin jami’an tsaro zuwa jihar, domin kare rayukan fararen hula da muhimman kayayyaki dake wurin.

Sanarwar ta kara da cewa, hukumar tsaron wadda ke karkashin jagorancin shugaban majalisar kasar Abdel Fattah Al-Burhan, ta kira wani taron gaggawa jiya Lahadi, don tattauna hare-haren da suka faru ranar Asabar a El Geneina.

Hukumar wadda ta kira wakilan mambobinta daga majalisar rikon kwaryar kasar, da majalisar gudanarwa da hukumomin tsaro, ta kuma yanke shawarar kafa wani kwamiti mai karfi, domin ya binciko harin na El Geneina, da gano tushen matsalar, kana ya mika shawarwarinsa, tare da gurfanar da wadanda suka aikata shi tare da hukunta wadanda ke da hannu a ciki. (Ibrahim)