logo

HAUSA

Sassa Daban Daban Na Afirka Sun Nuna Karfin Gwiwa Kan Yadda Rigakafin Kasar Sin Zai Taimakawa Nahiyar Wajen Yaki Da Annobar COVID-19

2021-01-18 16:12:40 CRI

Tun bayan barkewar annobar cutar numfashi ta COVID-19, kasar Sin take bai wa kasashen Afirka kayayyakin yaki da annobar, tare da tura musu likitoci, sa’an nan tana hada kai da wasu kasashen Afirka wajen nazarin allurar rigakafin cutar. Dangane da lamarin, sassa daban daban na Afirka sun yaba wa goyon bayan da kasar Sin take ba nahiyar.

Ahmed Ogwell, mataimakin darektan cibiyar kandagarki da dakile cututtuka masu yaduwa ta Afirka ya nuna cewa, kasar Sin tana taimakawa Afirka a wasu fannoni, tana bai wa kasashen Afirka shawarwari da goyon baya dangane da yaki da annobar. Cibiyarsa tana hada kai da takwararta ta kasar Sin, su yi musayar bayanai, a kokarin ganin kasashen Afirka sun kara yaki da annobar yadda ya kamata.

An fara yi wa al’umma allurar rigakafin cutar COVID-19 wanda kamfanin SINOPHARM na kasar Sin ya samar a kasar Seychelles a kwanan baya. Shugaban kasar Wavel Ramkalawan ya zama mutum na farko a kasar da aka yi wa allurar rigakafi na kasar Sin. Kafin wannan kuma, ya taba godewa kasar Sin bisa kayayyakin da ta bai wa kasarsa kan lokaci, wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen yaki da annobar a Seychelles. (Tasallah Yuan)

Tasallah Yuan