logo

HAUSA

An yi wa mataimakin shugaban kasar Turkiyya allurar riga-kafin cutar COVID-19 kirar kasar Sin

2021-01-17 17:25:44 CRI

An yi wa mataimakin shugaban kasar Turkiyya allurar riga-kafin cutar COVID-19 kirar kasar Sin_fororder_A

An yiwa mataimakin shugaban kasar Turkiyya Fuat Oktay allurar riga-kafin cutar COVID-19 wanda kasar Sin ta samar jiya Asabar a wani asibitin dake birnin Ankara, al’amarin da ya sa ya zama babban jami’in gwamnatin Turkiyya na uku da ya karbi allurar riga-kafin, baya ga shugaban kasar gami da ministan lafiyar kasar.

Rahotannin sun ce, mataimakin shugaban ya jaddada cewa, akwai mutane da yawansu ya tasamma dubu 700 wadanda aka yiwa allurar riga-kafin a kasar Turkiyya. Duk da cewa bada jimawa ba aka fara wannan aikin a kasar, amma adadin mutanen da suka karbi allurar yana kan gaba a duk fadin duniya baki daya. Yana kuma fatan Turkiyya zata fito da tata allurar a watan Afrilun bana. Mista Oktay ya kuma yi kira ga daukacin al’ummun kasar su karbi allurar, a cewarsa, wannan abu yana da matukar muhimmanci ga lafiyar dan Adam gami da farfadowar zaman rayuwar al’umma tun da wuri.

A ranar 13 ga wata, sashin kula da magunguna da kayan aikin jinya na ma’aikatar lafiya ta kasar Turkiyya ya sanar da amincewa da fara amfani da allurar riga-kafin cutar COVID-19 da kasar Sin ta samar.(Murtala Zhang)