logo

HAUSA

Dr. Sheriff Ghali Ibrahim: Kasar Sin tana bakin kokarinta wajen kare hakkin al'ummarta

2020-07-14 13:19:13 CRI

Dr. Sheriff Ghali Ibrahim: Kasar Sin tana bakin kokarinta wajen kare hakkin al'ummarta

Dr. Sheriff Ghali Ibrahim, malami ne dake koyarwa a sashin kimiyyar siyasa da huldar kasa da kasa a jami'ar Abuja ta Najeriya. A yayin zantawarsa da Murtala Zhang, Dr. Sheriff ya jaddada cewa, gwamnatin kasar Sin tana bakin kokarinta wajen kare hakkin dan Adam, ciki har da maida hankali kan kare tsaro da lafiyar al'umma, da taimaka musu wajen samun ci gaba.

Dangane da batutuwan da suka shafi yankunan Hong Kong da Taiwan da Tibet da kuma Xinjiang, Dr. Sheriff ya ce dukkan sassan mallakin kasar Sin ne, wadanda ba za'a iya balle su daga kasar ba. Kuma a iya saninsa, babu wani batun tauye hakkin dan Adam a wadannan wurare, sai dai kawai akwai wasu kasashen yammacin duniya wadanda suke amfani da batun hakkin al'umma domin fatattakar gwamnatin kasar Sin, da kuma shafa mata bakin fenti, domin kawo tsaiko ga ci gaban kasar.(Murtala Zhang)