Su Jianhua yana tsamani, hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka yana da kyakkyawar makoma a fannoni daban daban cikin shekaru masu zuwa. Ya ce, "Ina tsamani da farko ya kamata kasar Sin da kasashen Afirka suna iya kara yin hadin gwiwa kan makamashi. Na biyu shi ne aikin gona, yanzu kasashen duniya da yawa suna fuskantar matsalar aikin gona, amma kasashen Afirka suna da sharadi mai inganci kan aikin gona. Ban da haka kuma, ya kamata kasar Sin da kasashen Afirka su kara yin hadin gwiwa kan fannin hada-hadar kudi."
A karshe, Su Jianhua ya nuna cewa, dalilin da ya sa ya yi kokarin sa kaimi ga hadin gwiwar da ke tskanin kasar Sin da kasashen Afirka shi ne yana kaunar kasar Sin. Kuma yana son nuna godiya ga taimakon da matarsa ta kasar Sin ta yi masa. [Musa Guo] 1 2 3
|