Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-06 18:07:39    
Za a karfafa hulda tsakanin Sin da kasashen Afrika??Kai ziyara ga babban malami na sashen kula da dangantaka tsakanin kasa da kasa, da harkokin diplomasiya na jami'ar Nairobi

cri


Bisa kara raya dangantaka tsakanin Sin da kasashen Afrika, mutanen bangarorin biyu su ma suna kara yin cudanya. Mr. Garrishon ya ce, 'Tun daga shekara ta 2003, kasashen Sin da Kenya suna ta kara yin hadin kai a fannoni daban daban, musamman ma a fannin al'adu. A shekara ta 2005, an kafa kwalejin Confucius a jami'ar Nairobi. Wannan kwalejin ta Confucius na samar da wani dandali mai kyau ta fuskar koyon Sinanci ga daliban kasar Kenya. Yanzu, matasa masu yawa suna sha'awar koyon Sinanci, da al'adun kasar Sin.'

Mr. Garrishon ya ce, kasashen Afrika da yawa suna ganin cewa, kasar Sin wata kasa ce dake da karfin bunkasuwa. Dalilin da ya sa kasashen Afrika ke iya raya dangantakar hadin kai cikin dogon lokaci tare da kasar Sin, shi ne kasar Sin na nuna girmama ga 'yancin mulkin kai, da tsarin bunkasuwar sauran kasashe, kazalika kuma, ba ta tsoma baki cikin harkokin gida, a waje guda tana yin kokari da nufin samun bunkasuwa tare da kasashen waje ba tare da gitta sharuda ba, ra'ayinta game da harkokin diplomasiya yana da bambanci sosai da na kasashen yamma.
1 2 3