Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-05 14:36:03    
Za a gudanar da dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka

cri

Bisa labarin da aka bayar, an ce, kafin bude taron ministoci a karo na hudu, dadanlin tattaunawar zai yi taron manyan jami'ai a karo na 7 a ran 6 ga wata, da taron shugabannin kamfanonin Sin da kasashen Afirka mai taken "Neman samun bunkasuwa baki daya" a ran 7 ga wata. Firaminista Wen Jiabao zai halarci bikin bude taron domin yin jawabi.

Bayan haka, a wajen taron ministocin, bangarorin biyu za su yi nazari kan yadda aka tabbatar da sakamakon da aka samu a taron koli na birnin Beijing. Kuma za su zartas da "Sanarwar Sharm El Sheikh ta dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka" da "Shirin Sharm El Sheikh na dandalin hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu daga shekarar 2010 zuwa shekarar 2012". Dadin dadawa, gwamnatin Sin za ta shelanta sabbin matakan hadin gwiwa tsakaninta da kasashen Afirka.

Dandalin hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka jagora ce dake jagorancin bunkasuwar dangantakar sada zumunta tsakanin bangarorin biyu har zuwa lokaci mai tsawo. A wajen taron ministoci a karo na farko da aka yi a shekarar 2000, sun sanar da kafa sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare irin ta "moriyar juna mai dorewa da adalci cikin dogon lokaci". A shekarar 2003 kuma, a gun taron ministoci a karo na 2, Sin da kasashen Afirka sun ba da shawarar karfafa irin wannan dangantaka tsakaninsu. A gun taron koli na birnin Beijing da taron ministoci a karo na 3 da aka gudanar a shekarar 2006, shugabannin Sin da kasashen Afirka sun amince da kafa sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakaninsu baki daya.

Tun daga shekarar 2000 zuwa yanzu, dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka ya riga ya shafe shekaru 9 ana yinsa. A cikin wadannan shekaru 9, dangantaka tsakaninsu ta samu babban ci gaba. Musamman bayan shekarar 2006 da aka yi taron koli na Beijing, hadin gwiwar sada zumunta tsakaninsu ya kai wani sabon mataki. Sin tana kokarin kulla sabuwar dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare tsakaninta da kasashen Afirka irinta "amincewa da juna a fannin siyasa, da hada gwiwa da cin moriyar juna a fannin tattalin arziki, da musayar fasahohi a fannin al'adu". A sabili da haka, hadin gwiwa tsakaninsu ya taka rawa a zo a gani a duniya.

1 2 3