Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-04 22:05:53    
  Jami'an gwamnatin Kenya da na Sin suna dokin kiran taron dandalin tattaunawar hadin kan kasar Sin da Afrika

cri

Yayin da ya ke hira da wakilin gidan rediyonmu, ministan shari'a da harkokin tsarin dokokin mulkin kasa Mr Mutula Kilonzo ya bayyana fatansa na karfafa hadin kan Kenya da kasar Sin a fannin aikin gona da ciniki. Ya ce "muna so mu bunkasa cinikayya,muna fatan dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika ta yi ta samun cigaba,muna fatan za a tattauna wasu muhimman batutuwa a gun taron nan,musamman batun aikin gona.Mun gano cewa fadin gona ga kowane basine kadan ne,amma kasar Sin ta iya ciyar da kanta da isashen abinci har ma ta sayar da wasu ga kasashen ketare. Ga kowanenmu yana da fadin kasa da ya fi na kowane basine yawa sosai,amma mu kan yi fama da karancin abinci. Muna so mu fahimci da matakan da jam'iyyar kwaminis ta Sin ta dauka wajen samar da isashen abinci ga mutanenta a cikin shekaru 30 da suka shude.A fannin cinikayya 'yan kasuwa na Kenya suna da dama da yawa na fitar da kayayyakinsu zuwa kasar Sin, kuma mun shigo da kayayyakin sadarwa da sauran kayayyaki daga kasar Sin. Muna so mu san wane mataki ne kasar Sin ta dauka har ta samu saurin cigaban tattalin arziki."

Tsohon jakada na kasar Kenya a Sin Mr Jabil Habib ya yaba da tsarin dandalin tattaunawa kan hadin kan Sin da kasashen Afrika. A ganinsa samun nasara tare cikin hadin gwiwa shi ne ainihin hadin kan kasar Sin da kasashen Afrika. (Ali)


1 2 3