Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-04 22:05:53    
  Jami'an gwamnatin Kenya da na Sin suna dokin kiran taron dandalin tattaunawar hadin kan kasar Sin da Afrika

cri

Bisa labarin da aka samu, an ce a gun taron ministoci na dandalin tattaunawa kan hadin kan kasar Sin da Afrika da za a yi, Sin da Afrika za su kimanta ci gaban da aka samu a dukkan fannoni wajen tabbatar da hadin kan kasar Sin da kasashen Afrika bayan taron koli na Beijing,kuma za su kara bayyana alkibla da za a bi wajen bunkasa dangantaka dake tsakanin Sin da kasashen Afrika da tsara shirin hadin kan Sin da kasashen Afrika a fannoni daban daban cikin shekaru uku masu zuwa. Mataimakin shugaban kasar Kenya Kalonzo Musyoka ya yaba da ci gaban hadin kan Sin da kasashen Afrika da aka samu ya ce " Daga huldodin dake tsakaninta da daukacin Afrika, mun gano cewa kasar Sin amintacciyar aminiya ce ga kasashen Afrika,duk girmar kasa ko kasamarta,kasar Sin tana mutunta dukkan kasashen duniya,ba ta tsolma bakinta cikin harkokin gida na sauran kasashe.muna farin ciki da ganin ci gaban dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika,muna fatan taron nan zai samu cikakkiyar nasara."

Jakadan kasar Sin dake a kasar Kenya Mr Deng Hongbo ya bayyana cewa a cikin shekaru biyu na baya,dangantaka dake tsakanin Sin da Afrika ta samu babban cigaba. Taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawa kan hadin kan Sin da Afrika zai samar da wata dama ga kasar Sin da Afrika da su kara tattauna matsayar bai daya da suka samu a taron koli na Beijing. Ya kuma bayyana makasudin taron da cewar " a gun taron da za a yi Sin da Afrika za su tattauna muhimman batutuwan da suke da muhimmanci sosai ga Afrika ciki har da aikin gona da samun isashen abinci da kuma kara yin manyan ayyuka. Ina fatan wasu sabbin manufofin siyasa na kasar Sin za su taimakawa wajen samar da tallafi ga kasashen Afrika da inganta dangantaka dake tsakanin bangarorin nan biyu. Da haka na hakikance cewa taron nan da za a yi taro ne na daukaka ci gaban hadin kan Sin da kasashen Afrika kuma zai sami nasara."

1 2 3