Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-04 17:29:44    
Yankin yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Zambia yana da kyakkyawar makoma a cewar ministan kasuwanci na kasar Zambia

cri

Mr. Mutati ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Zambia za ta daidaita dokokin da abin ya shafa domin ba da taimako ga yunkurin gina karamin yankin raya tattalin arziki na Lusaka. Ban da haka kuma, ya fayyace cewa, za a fara gina hanyar da ke hada da filin jirgin sama na duniya na Lusaka da wannan yankin raya tattalin arziki na Lusaka.

Mr. Mutati ya ce, a "taron ciniki da zuba jari na kasa da kasa a karo na 13 na kasar Sin" da aka yi a birnin Xiamen da ke kudancin kasar Sin, ya fadakar da kamfannonin kasar Sin kan yankin raya tattalin arziki na Zambia domin jawo karin jari. A sa'i daya kuma, yana fatan wannan yanki zai ci gaba jawo hankali na kamfanin Zambia da na sauran kasashen duniya, kuma wannan yanki zai zama wani yankin raya tattalin arziki na kasa da kasa.

Kasar Zambia tana tsakiya maso kudancin nahiyar Afirka, tana da yawan mutane miliyan 11.7. Yawan tagulla da ta haka ya zama na hudu a duniya. A dogon lokacin suka wuce, kasar Zambia tana da matsalar tsarin tattalin arzikin mai sauki, tana dogara kan masana'antun haka kwal. Yanzu, kasar Zambia tana kokarin kyautata tsarin tattalin arziki ta hanyoyi daban daban. [Musa Guo]


1 2 3