Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-04 17:29:44    
Yankin yin hadin gwiwa tsakanin kasashen Sin da Zambia yana da kyakkyawar makoma a cewar ministan kasuwanci na kasar Zambia

cri

Bayan shekaru biyu da suka wuce, yanzu ana yin ayyukan gina manyan gine-gine da aikin neman 'yan kasuwa da jawo jari yadda ya kamata. Ya zuwa yanzu, wannan yanki ya riga ya karbi kamfannoni 13 daga kasashen Sin da Zambia. Yawan kudin da aka zuba ya kai fiye da dolar Amurka miliyan 800, yanzu an riga an zuba jari na dolar Amurka miliyan 550 da ke cikinsu, wannan ya samar da guraban aikin yi fiye da dubu 4 ga kasar Zambia. Ban da haka kuma, a ran 15 ga watan Janairu na sheakrar 2009, shugaba Rupiah Banda na kasar Zambia da ministan kula da harkokin ciniki Chen Deming sun halarci bikin bude karamin yankin raya tattalin arziki a Lusaka.

Mr. Mutati ya ce, "A watan Yuli na shekarar bana, bisa gayyatar da ma'aikatar harkokin ciniki ta kasar Sin ta yi, na je kasar Sin na halarci kos na horar da ministocin kasar Zambia wajen gina yankin raya tattalin arziki. Na kai ziyara ga yankunan raya tattalin arziki da dama, na yi mamaki kan nasarorin da suka samu. Na yi imanin yankin raya tattalin arziki na kasar Zambia zai ci nasara."

1 2 3