Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-03 21:07:11    
Dandalin FOCAC ya samar da wata dama mai muhimmanci ta yadda za a raya huldar da ke tsakanin Sin da Afirka sosai

cri

'A fannin siyasa, kasar Sin da kasashen Afirka sun hada kansu sosai, inda su kan rufa wa juna baya yayin da suke kula da harkokin kasa da kasa. Ban da wannan kuma, yawan kayayyakin da ake saye da sayarwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka yana ta karuwa cikin sauri, wanda ya zarce dala biliyan 100 a shekarar 2008. Sa'an nan a fannonin hada-hadar kudi da yawon shakatawa, bangarorin 2 sun kara hada gwiwa. Shi ya sa za mu iya cewa, an aiwatar da manufafi 8 na tallafawa kasashen Afirka da kyau.'

Bayan haka kuma, Zhang Ming ya jaddada cewa, duk da cewa an samu barkewar rikicin hada-hadar kudi, wanda ya yi illa ga tattalin arzikin kasashen duniya, amma, kamfanonin kasar Sin ba su taba rage yawan jarin da suke zubawa kasashen Afirka ba, sa'an nan an ci gaba da kokarin inganta hadin gwiwar da ke tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Kamar yadda Zhang ya ce, 'Tun daga shekarar bara, rikicin hada-hadar kudi ya barke, wanda ya samar da mummunan tasiri ga kasashen duniya, haka ma rikicin yake wa kasar Sin. Amma, duk da haka, gwamnatin kasar Sin ta ci gaba da sa kaimi ga kamfanonin kasar, don su kara zuba jari a Afirka, ta yadda za a taimaka wajen raya nahiyar. Sa'an nan gwamnatin kasar Sin ta yi alkawarin cewa, kamfanonin kasar Sin da ke nahiyar Afirka ba za su rage yawan ma'aikata ba, kuma ba za su janye jarin da suka zuba ba.'

1 2 3