Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-03 21:07:11    
Dandalin FOCAC ya samar da wata dama mai muhimmanci ta yadda za a raya huldar da ke tsakanin Sin da Afirka sosai

cri

Masu sauraro, ko kuna sane da cewa, daga ranar 8 zuwa ranar 9 ga watan Nuwamba, za a shirya taron ministoci na karo 4 na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afirka na FOCAC a birnin Sharm ei-Sheikh, shahararren wurin shakatawa na kasar Masar, wanda zai zama wani taro mai muhimmanci da ya biyo bayan taron koli na dandalin FOCAC da aka shirya a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin, a shekarar 2006. Sa'an nan, Zhang Ming, darekatan sashen Afirka na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ya yi bayani kan yadda za a shirya taron, da kuma nasarorin da kasashen Afirka da kasar Sin suka samu lokacin da suke kokarin yin hadin gwiwa da ke tsakaninsu.

Kamar yadda Zhang ya ce, akwai manyan ayyuka 2 da za a yi a wajen taron. 'Aiki na farko shi ne, tantance yadda aka gudanar da manufofin da aka samar a wajen taron koli na dandalin FOCAC da aka shirya a birnin Beijing , sa'an nan aiki na biyu shi ne, samar da shiri kan yadda za a hada kan kasashen Afirka da kasar Sin cikin shekaru 3 masu zuwa.'

A gun taron koli da aka yi a Beijing a shekarar 2006, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya sanar da manufofi 8 da gwamnatin kasar Sin ta yi alkawarin daukansu don tallafawa kasashen Afirka, wadanda aka aiwatar da su yadda ya kamata, in ji Zhang Ming, darektan sashen Afirka na ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin.

1 2 3