Ra'ayin bainal jama'a sun yi hasashen cewa, janye jiki daga zaben da Mr. Abdullah ya yi ya sa halin siyasa da kasar Afghanistan ke ciki ya sake shiga hali mai sarkakkiya, kuma halin tsaro mai tsanani zai ci gaba da zama kalubale mafi tsanani na zagaye na biyu na zaben. A cikin zagayen da ya gabata, kungiyar Taliban ta haddasa al'amuran tashe-tashen hankula fiye da 200 a duk fadin kasar, wadanda suka yi sanadiyar mutuwar mutane a kalla 26. Sakamakon tabarbarewar halin tsaro, yawan mutanen da suka kada kuri'a ya kai kashi 38.7 cikin kashi dari kawai bisa na duk kasar. Bayan da kwamitin zabe mai zaman kansa na kasar Afghanistan ya sanar da shirya zagaye na biyu na babban zaben, kungiyar Taliban ta sake yin barazanar cewa, bai kamata ba a kada kuri'a a cikin zaben, ya kamata a yi dagiya da shi. Dukkan wadanda suka mutu ko suka ji raunuka sakamakon kada kuri'a su kansu za su dauki alhaki a wuyansu. Sabo da haka manazarta sun nuna cewa, watakila yawan mutane da za su kada kuri'a a cikin zagaye na biyu na zaben zai ragu.(Kande Gao) 1 2 3
|