Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-02 21:43:47    
Dan takarar shugaban kasar Afghanistan Abdullah Abdullah ya janye jiki daga zagaye na biyu na babban zabe

cri

Bisa kwarya-kwaryar kidayar kuri'u da kwamitin zabe ya bayar a ran 16 ga watan Satumba na bana, an ce, yawan kuri'un da shugaban kasar Afghanistan na yanzu Hamid Karzai ya samu ya kai kashi 54.6 cikin kashi dari a cikin babban zaben da aka yi a watan Agusta. Amma Mr. Abdullah ya yi zargin cewa, akwai batun magudi a cikin zaben. Daga baya kuma kwamitin kula da kararrakin zabe da ke karkashin jagorancin MDD ya fara yin bincike kan batun. A ran 20 ga watan jiya, kwamitin zabe mai zaman kansa na kasar Afghanistan ya sanar da cewa, bisa rahoton da kwamitin sauraran karar zabe ya bayar, an ce, yawan kuri'un da shugaba Karzai ya samu ya kai kashi 49.67 cikin kashi dari. Sakamakon kasancewar babu dan takara da ya samu rabin yawan kuri'u, bisa tsarin mulkin kasar Afghanistan, 'yan takara biyu da ke kan gaba za su shiga zagaye na biyu na babban zaben a ran 7 ga wata. Daga baya kuma a ran 26 ga watan jiya, Mr. Abdullah ya ba da shawarar tube shugaban kwamitin zaben da ministoci guda uku wadanda ke da hannu a cikin batun magudi a zagaye na farko na babban zaben daga mukamansu don zama sharadinsa na shiga zagaye na biyu na zaben. Amma shugaba Karzai ya mayar da martani kan cewa, Mr. Abdullah ba shi da ikon tsoma baki kan sallamar 'yan majalisar minisoticn kasar. Game da batun janye jiki da Mr. Abdullah ya yi, kakakin shugaba Karzai a fannin takarar neman zaben ya bayyana a ran nan, cewar ya yi bakin ciki sosai kan batun, amma za a yi zagaye na biyu na zaben bisa shirin da aka tsara a da.

1 2 3