Mista Jiao Guoli, kwararre ne a fannin ayyukan soja na kasar Sin ya nuna cewa, a yayin mu'amala da cudanyar da aka yi kwanan baya tsakanin sojojin Sin da Amurka, ra'ayoyin da kasar Amurka ta nuna kan kasar Sin sun samu sauye-sauye:
"Yanzu akwai manyan jami'an soja na kasar Amurka wadanda suka bayyana cewa, kasar Sin ba abokiyar gabar kasar Amurka ba ce, haka kuma rundunar sojanta ba runduna ba ce wadda ke kawowa Amurka barazana. Ana maraba da samun sauye-sauyen ra'ayoyin da manyan jami'an sojan Amurka ke nunawa a kan kasar Sin."
Ko da yake an samu sakamako mai kyau a ziyarar, amma bangarorin Sin da Amurka ba su samu ra'ayi daya ba a kan wasu batutuwa, ciki kuwa har da sayarwa yankin Taiwan makamai da Amurka ke yi. Wani kwararre a fannin ayyukan soja, wanda kuma shehun malami ne a cibiyar nazarin manyan tsare-tsare ta jami'ar koyon ilimin tsaron gida ta kasar Sin Mista Meng Xiangqing yana mai ra'ayin cewa, ya kamata bangarorin biyu su kara samun fahimtar juna: "Da farko, wato a inganta samun fahimtar juna a manyan tsare-tsare, kasar Amurka ta dade tana nuna kokwanto dangane da bukatar kasar Sin ta fannin raya kasa. Na biyu kuwa shi ne, akwai wasu dokokin da kasar Amurka ta tsara wadanda suke jawo tsaiko ga mu'amalar da ake yi tsakanin Sin da Amurka ta fannin harkokin soja. Amma abun dake gaba da kome shi ne, batun yankin Taiwan, sayarwa Taiwan makamai babbar matsala ce."
1 2 3
|