Bisa goron gayyatar da ministan tsaro na kasar Amurka Robert Gates ya ba shi, mataimakin shugaban kwamitin soja na tsakiya na kasar Sin Janar Xu Caihou ya fara ziyara a kasar Amurka tun daga ranar 24 ga watan Oktoba zuwa ranar 3 ga watan Nuwamba. Wannan dai shi ne karo na farko da wani shugaba na kwamitin soja na tsakiya na kasar Sin ya kai ziyara Amurka bayan da Barack Obama ya hau karagar mulkin kasar. Kwararrun kasar Sin a fannin harkokin soja na ganin cewa, ziyarar Xu Caihou a wannan gami zata taimaka wajen ci gaba da raya dangantakar sojojin kasashen Sin da Amurka.
Sakamakon kokarin da shugabannin rundunonin soja na kasashen Sin da Amurka suka yi, an cimma dimbin nasarori a yayin ziyarar Mista Xu Caihou a Amurka. Kasashen biyu sun cimma daidaito a manyan fannoni 7, ciki kuwa har da gudanar da ayyukan ceto bisa ra'ayin jin-kai, da yaki da ta'addanci, da tabbatar da tsaro a kan teku, da horas da matasa jami'an soja, da gudanar da atisayen soja a kan teku da sauransu.
1 2 3
|