Ko da yake nisan da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka ya kai fiye da kilomita dubu 10, amma zumuncin da ke tsakaninsu ya dade. Fararen hula da yawa da suka kai ziyara ga ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin a ran 31 ga watan Oktoba su ne sun taba yin aiki a kasashen Afirka, kuma sun iya shaida yadda ake raya huldar sada zumunta irin ta hadin gwiwa a tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka. Wasu daga cikinsu suka taba yin aikin shimfida hanyar dogo da ta hada kasashen Tanzania da Zambiya yau kusan shekaru 40 da suka gabata, wasu daga cikinsu likitoci ne da suka yi aiki a kasashen Afirka. Mr. Li Yun, wani likita ne da ke aiki a asibitin Xuanwu na Beijing ya taba yin aiki a kasar Guinea. Lokacin da yake tunawa da ranakun da yake aiki a Guinea, an ta da hankalinsa sosai kuma ya ce, "Ni shugaba ne na kungiyar likitoci da kasar Sin ta tura zuwa kasar Guinea a karo na 20. A watan Agusta na shekara ta 2008, mun dawo nan kasar Sin daga kasar Guinea. Kungiyoyin likitoci na kasar Sin sun riga sun yi shekaru 40 ko fiye suna ba da aikin jiyya a kasashen Afirka. A cikin wadannan shekaru 40 ko fiye da suka gabata, mun ba da aikin jiyya ga miliyoyin marasa lafiya na kasashen Afirka, kuma mun sada zumunci a taskaninmu da jama'ar Afirka, har ma mun samu yabo da girmamawa daga wajensu. Mu manzanni ne da ke sanya farar riga, mun kuma kasance tamkar 'yan diflomasiyya."
A karshen bikin bude kofar ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ga fararen hula da aka yi a ran 31 ga watan Oktoba, wasu daliban kasashen Afirka da suke karatu a kasar Sin sun taka rawa mai suna "shagali mai farin ciki", inda wani dalibi ya yi amfani da harshen Sinanci ya yi ihu da cewa, "Amincin da ke tsakanin Sin da kasashen Afirka yana nan har abada!" (Sanusi Chen) 1 2 3
|