
A karshen wannan mako, wato ran 8 ga wannan wata, za a kaddamar da taron ministoci a karo na 4 na wannan dandalin a Sharm el Sheikh na kasar Masar da aka saba shiryawa a duk shekaru uku-uku. Firayin ministan kasar Sin Wen Jiabao da wasu shugabannin kasashen Afirka za su halarci bikin kaddamar da wannan taro, kuma zai bayar da wani muhimmin jawabin da ke kunshe da sabbin matakan da kasar Sin za ta dauka domin kara yin hadin gwiwa a tsakaninta da kasashen Afirka.
1 2 3
|