Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-11-02 16:44:21    
Ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta bude kofarta ga fararen hula

cri

A ran 31 ga watan Oktoba da yamma, ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin ta bude kofarta ga fararen hula domin dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. Fararen hula fiye da dari daya na kasar Sin sun shiga zauren ma'aikatar domin sanin wakoki da raye-raye da sauran al'adun Afirka da kuma yadda ake yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Bisa amon raye-raye na Afirka da kungiyar wakoki da raye-raye ta kasar Uganda ta yi, Mr. Yang Jiechi, ministan harkokin waje na kasar Sin da jakadun kasashen Afirka 33 da ke nan kasar Sin sun shiga dakin watsa labaru tare, inda suka kuma halarci bukukuwan da aka yi domin fararen hula game da dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. Lokacin da yake bayar da jawabi, Mr. Yang ya ce, kasar Sin da kasashen Afirka sun kafa dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakaninsu a shekara ta 2000 domin neman ci gaba da kuma tinkarar kalubaloli cikin hadin gwiwa. Ya ce, "Bangarorin Sin da kasashen Afirka suna amfani da wannan dandali wajen yin musayar ra'ayoyinsu sosai kan huldar da ke tsakaninsu da batutuwan kasa da kasa da na shiyya-shiyya da suke jawo hankalinsu tare domin daidaita matsayin da suke dauka da kara goyon bayan juna. Yanzu wannan dandali ya riga ya zama wani sannanen samfuri a duniya da ke nuna yadda kasar Sin da kasashen Afirka suke raya hadin gwiwa irin ta sada zumunta, yana kuma jawo hankalin sauran kasashen duniya sosai. Haka kuma, wannan dandali ya zama wani abin koyi a fannin kara yin hadin gwiwa a tsakanin kasashe maso tasowa, har ma ya jawo sauran kasashen duniya da su kara mai da hankali kan Afirka da kuma kara zuba jari a Afirka."

1 2 3