Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-21 14:38:56    
Za a yi zaben shugaban kasa a zagaye na biyu a kasar Afghanisan

cri

A ganin kafofin yada labarai na wurin Hamid Karzai ya gamu da matsin lamba mai karfi daga kasashen yamma. Gamayyar kasa da kasa ta yi maraba da zaben shugaban kasa a zagaye na biyu da za a yi a kasar Afghanistan. Babban sakatare na majalisar dinkin duniya Ban Ki-moon ya alkawarta cewa majalisar dinkin duniya za ta ba da karin taimako ga zabe na zagaye na biyu da za a yi. Firayim ministan Britaniya Gordon Brown da shugaban kasar Amurka Barack Obama sun yi maraba da kudurin hukumar zabe mai zama kanta ta Afghanistan na yin zabe a zagaye na biyu. Obama ya ce abu mafi a'ala ga Afghanistan a halin yanzu,shi ne mutanenta za su hada kai wajen sa kaimi don yunkurin shimfida dimakuradiya da zaman lafiya. Masu binciken al'amura suna masu ra'ayi cewa a yayin da Barack Obama ke tunanin tura karin sojojin zuwa kasar Afghanistan,ci gaban da aka samu a halin da kasar Afghanistan ke ciki zai taimaka wa Obama da ya gaggauta tsaida kuduri kan batun tura karin sojojin. Masu binciken al'amuran sun yi hasashe cewa Karzai yana da magoya baya da suke fi yawa tskanin kabilarsa ta Pushito wadda ta fi yawan mutane a kasar Afghanistan,kila zai sake samun nasara a zagaye na biyu. A birnin Kandahar inda magoya bayan Karzai suka fi yawa,magoya bayansa sun bayyana cewa za su yi kira ga mutanensu da su fito don jefa kuri'a ta yadda Karzai zai samu kuri'un da suka fi yawa bisa na zagaye na farko. (Ali)


1 2 3