
A ran 20 ga watan Augusta an yi zaben shugaban kasa a karo na biyu bayan da aka kada hukumar mulki ta Taliban a kasar Afghanistan,bisa kwarya-kwaryar sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta ta bayar a ran 16 ga watan Satumba, an ce Hamid Karzai ya samu kashi 54.6 bisa dari na yawan kuri'un da aka kada. Duk da haka ana tababar da kasancewar alamun magudi a zaben da aka gudanar,kwamitin kula da kararraki na Afghanistan da majalisar dinkin duniya ke jagoranta ya tantance kuri'un da aka kada,a ran 19 ga watan Oktoba ya bayyana cewa an tafka magudi a tashoshin zabe 210 don haka yanzu an mai da kuri'unsu sun zama banza,ya bukaci hukumar zabe mai zama kanta ta Afghanistan ta gyara sakamakon. Bisa kididdigar da hukumar kula da kararrakin zabe ta yi,an ce kri'un da Karzai ya samu ba su kai kashi hamsin cikin dari na yawan kuri'un da aka kada ba. Kafin wannan Karzai ya yi adawa da a yi zabe a zagaye na biyu.Amurka da kasashen yamma sun nace a kan a shiga zagaye na biyu ko a kafa gwamnatin hadin gwiwa da ta hada Karzai da abokin hammayarsa Abdullah Abdullah.A makon da ya gabata,manyan jami'an Amurka da na Faransa sun kai ziyara bi da bi a birnin Kabul sun yi kokarin sulhuntawa kan takaddamar zabe.
1 2 3
|