Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-08 19:50:34    
Ana ci gaba da fama da halin rashin tabbas a kasar Madagascar

cri

Na biyu kuwa, firaminista mai ci yanzu, Monja Roindefo, ya taka muhimmiyar rawa a juyin mulkin da aka yi a watan Maris na wannan shekara, haka kuma yana mai fada a ji cikin magoya bayan Rajoelina. Kasancewarsa mai tsattsauran ra'ayi da ke cikin magoya bayan Rajoelina, har kullum yana kin yarda da Rajoelina ya yi rangwame na kowane iri. A sabo da haka, ko Rajoelina ya sami amincewa daga Roindefo da magoya bayansa wajen sake firaministan wucin gadi?

Ban da haka, daidaito ne kawai aka cimma a maimakon yaryeyeniya. An ce, a cikin kwanaki masu zuwa, shugabannin jam'iyyun siyasa hudu na kasar ta Madagascar za su yi shawarwari a birnin Geneva ko kuma Paris, inda a hukunce ne za su daddale yarjejeniyar raba madafun iko. To, ko za a daddale yarjejeniyar ba tare da samun wata matsala ba? A cikin shekaru fiye da 10 da suka wuce, kusan duk juyin mulkin da aka yi ya kan haddasa rikicin siyasa mai tsanani, kuma bangarori daban daban sun daddale yarjejeniyoyi da dama kan yunkurin daidaita rikicin, amma kalilan ne aka tabbatar da su.

A cikin irin wannan hali ne, manzon musamman na tarayyar Afirka, Ablasse Ouedraogo wanda ya halarci shawarwarin da aka yi a ran 6 ga wata, ya ce, dole ne shugabannin jam'iyyun Madagascar su nuna hikimarsu da burinsu na yin iyakacin kokarin hada gwiwa da juna kafin zaben da za a gudanar, a maimakon su ci gaba da ka-ce-na-ce a kan maganar raba madafun iko.(Lubabatu)


1 2 3