
Daidaiton da jam'iyyun hudu suka cimma ya kawar da babban abin da ya hana ruwa gudu wajen samun sulhun siyasa a kasar ta Madagascar, amma duk da haka, ba za a iya kyautata hasashe kan makomar siyasa a kasar ba, duk sabo da shakkun da jama'a ke da su.
Na farko, a ran 6 ga wata da dare, kakakin Marc Ravalomanana tsohon shugaban kasar ya ce, dalilin da ya sa jam'iyyu daban daban suka iya cimma daidaito a kan raba mafadun iko shi ne, da akwai wani babban sharadi, wato Andry Rajoelina ba zai tsaya takarar babban zaben da za a gudanar kafin karshen shekara mai zuwa ba. Amma har zuwa yanzu, Rajoelina bai mayar da martani a kan wannan bayani ba. Kasancewarsa shugaba mai ci yanzu, ko zai iya yin watsi da ikon da ke hannunsa?
1 2 3
|