
Amma kafofin watsa labarai suna ganin cewa, sassaucin da kasar ta Iran ta yi a ranar 4 ga wata ba zai kai ga warware matsalar nukiliyarta ba. Akwai manyan bambance-bambance a tsakanin Iran da Amurka, kuma a tsakanin Iran da kasashe 6 masu halartar shawarwari kan batun nukiliyar kasar. Alal misali, ko da yake Iran ta amince da a gudanar da bincike kan masana'antar tace sinadarin Uranium ta biyu, amma ba ta nuna amincewa ba ga jami'an hukumar IAEA na su gudanar da ayyukansu ba tare da wani sharadi ba. Sabon rahoton da hukumar IAEA ta fitar ya nuna cewa, har zuwa yanzu akwai wasu muhimman batutuwan da ake bukatar Iran ta yi bayani. Game da haka, shugaban hukumar IAEA Mohamed El Baradei ya ce, kafin jami'an hukumar su gudanar da bincike kan masana'antar tace sinadarin Uranium ta Fordo, shugaban kungiyar kula da makamashin nukiliya ta Iran Ali Akbar Salehi zai kai ziyara ga hedkwatar hukumar IAEA a Vienna, babban birnin kasar Austria a ranar 19 ga wata. A wancan lokaci, kasashen Amurka da Rasha da Faransa gami da Iran za su gudanar da shawarwari kan yiwuwar mika aikin tace sinadarin Uranium da Iran ke yi ga sauran kasashe.(Murtala) 1 2 3
|