A ranar 25 ga watan Satumba, shugaban kungiyar kula da makamashin nukiliya ta Iran Ali Akbar Salehi ya sanar da cewa, Iran tana kokarin raya masana'antarta ta biyu ta tace sinadarin Uranium. Rahoto daga kafofin watsa labaran kasar ya ce, an soma gina wannan masana'anta ne tun shekara ta 2006, wadda ke cikin wani kauye mai suna Fordo a wani daji, mai tazarar kilomita 50 kudu da birnin Qom. A halin yanzu dai, an kusan kammala ayyukan gina wannan masana'antar tace sinadarin Uranium, amma har yanzu ba'a kafa na'urorin tace sinadarin ba. Da akwai rahotannin da suka bayyana cewa, yawan na'urorin tace sinadarin Uranium a masana'antar Fordo ba zai zarta na masana'antar tace sinadarin Uranium ta Natanz ba. Yanzu kasar Iran ta kafa na'urori kimanin 7000 domin tace sinadarin Uranium a masana'antar Natanz.
Har yanzu dai ba'a sani ba ko Iran ta fitar da bayanai kan masana'antarta ta biyu a fannin tace sinadarin Uranium ne a sanadiyyar matsin lamba da aka yi mata, amma ana tsammanin cewa, Iran ta nuna hazaka wajen warware wannan batu, haka kuma Mohamed El Baradei ya yi maraba da hadin-kai da Iran ke bayarwa a kan batun nukiliya.
1 2 3
|