Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-01 20:31:47    
Gagarumin biki yana sheda nasarar da kasar Sin ta samu

cri

Ma iya cewa, ana iya fahimtar bunkasuwar wata kasa daga wajen ci gabanta a fagen fasahar aikin soja. Ta haka, kasaitaccen biki da aka yi a babban filin Tian'anmen a ran 1 ga wata na da ma'ana mai zurfi. Qin Xiaoying, wani fitacce a kasar Sin ya nuna cewa, "Kasaitaccen maci da aka yi cikin fara'a domin murnar cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin ya karfafa zukatan mutane sosai, kuma ya taka muhimmiyar rawa wajen hada kan mutane da tabbatar da ganin kasar Sin ta ci gaba da samun bunkasuwa yadda ya kamata a nan gaba."

E, ya kamata Sinawa su yi alfahari da cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar mahaifarsu kasar Sin. A cikin shekaru 60 da suka wuce, kasar Sin ta zama wata muhimmiyar kasa a duniya, a maimakon wadda ke fama da tsananin talauci. Ta kama hanyar samun farfadowa. Haka kuma, tana kara yin babban tasiri ga duniya gaba daya. Yanzu gwamnatin Sin na waiwayar sakamako da fasahohin da ta samu a cikin shekaru 60 da suka wuce, sa'an kasashen duniya na zura ido kan makomar wannan kasa.

Kamar yadda shugaban kasar Sin ya fada, Sin da kasashen duniya ba za su iya rabuwa da juna ba. Yau a babban filin Tian'anmen, shugaba Hu Jintao na kasar Sin ya yi alkawari a hukumance da cewa, nan gaba nasarorin Sin za su kawo wa duniya karin moriya. Inda ya ce, "Jama'ar Sin na da karfin zuciya da kuma kwarewa wajen raya kasarsu yadda ya kamata, kana haka suke a fannin bai wa kasashen duniya gudummawarsu" (Sanusi Chen, Tasallah)


1 2