Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-10-01 20:31:47    
Gagarumin biki yana sheda nasarar da kasar Sin ta samu

cri

Ran 1 ga watan Oktoba, wata rana ce ta musamman ga Sinawa.

A ran 1 ga watan Oktoba na shekarar 1949, a ginin Tian'anmen da ke cibiyar birnin Beijing, Mao Zedong, marigayi shugaban kasar Sin na wancan lokaci ya sanar da kafuwar sabuwar kasar Sin, wato Jamhuriyar Jama'ar Sin. Bayan shekaru 60 da suka gabata, a wannan rana, kuma a ginin Tian'anmen na birnin Beijing, kasar Sin ta kuma shirya bikin duba faretin sojoji da shagalin yin maci cikin fara'a domin tunawa da wannan muhimmiyar rana.

Da karfe 10 na safe na ran 1 ga watan Oktoba, agogon Beijing, da farko, an yi jerin harbe-harben igwa har sau 60 a filin Tian'anmen domin alamta cika shekaru 60 da kafuwar sabuwar kasar Sin. Kuma a hukunce a kaddamar da babban taron taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin.

Shugaban kasar Sin Hu Jintao ya shiga mota mai samfuri Jar Tuta kirar kasar Sin ya bi titin Chang'an da aka gyara shi kwanan baya ya soma duba faretin sojoji daga yamma zuwa gabas.

Bayan shugaba Hu Jintao ya gama duba faretin sojoji, a karkashin jagorancin faretin ban girma na rukunin sojojin kasa da na sama da na ruwa na rundunar sojan 'yantar da jama'ar Sin da yake tsaron tutar kasar Sin, rundunoni 56 sun wuce ta cibiyar filin Tian'anmen domin shugabannin kasar Sin su duba faretinsu. Wannan ne karo na 14 da aka duba faretin soja a sabuwar kasar Sin.

A cikin wadannan rukunoni 56, akwai rukunoni 30 da suka yi nune-nunen makaman zamani iri iri da ake da su a rundunar sojan 'yantar da jama'ar Sin. A waje daya, jiragen sama na yaki, ciki har da jiragen sama masu saukar ungulu da jagaren sama masu dakon mai don sauran jigaren sama da aka rarraba su rukunoni 12 sun kuma ratsa sararin sama na filin Tian'anmen bi da bi.

A wannan rana, filin Tian'anmen ba kawai wani wurin duba faretin soja ne ba, ya kasance kuma wuri ne da aka nishadantar da jama'a.

Bayan da aka yi mintoci 66 ana duba faretin soja, jama'a sun soma yin maci cikin fara'a. Bisa taken waka mai suna "yaba wa jar tuta", matasa 1949 sun wuce gaba tare da wata babbar jar tutar kasar Sin. Jama'a dubu 100 da suke wakiltar bangarori daban daban da motoci masu launuka 60 da aka kawata su da kayayyaki daban daban sun kuma wuce filin Tian'anmen.

Jama'a masu sauraro, bikin duba faretin soja da macin da jama'a suka yi a filin Tian'anmen, gagarumin biki ne da aka yi domin taya murnar cika shekaru 60 da kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, shi ne kuma gagarumin biki na dukkan Sinawa baki daya.

Ga Sinawa, idan ka samu damar halartar bikin a filin Tian'anmen, sana'a ne a gare ka. A gun dandalin kallon bikin, Mr. Wei Jinsheng, mai ba da shawara a majalisar gudanarwa ta kasar Sin ya zura idonsa sosai kan sabbin na'urorin soja da suke wucewa a filin Tian'anmen. Yana cike da alfahari sosai ga karfin tsaron kasa da ake nunawa. Mr. Wei ya ce, "Lokacin da aka shirya bikin taya murnar cika shekaru 50 da kafuwar sabuwar kasar Sin, na taba kallon bikin. Idan an kwatanta wannan biki da na bikin da aka shirya yau shekaru 10 da suka gabata, akwai bambanci sosai. Na'urori da makamai iri iri da muke amfani da su dukkansu sun samu ci gaba kwarai. Sun shaida cewa, rundunar sojan 'yantar da jama'ar Sin rundunar soja ce mai karfi sosai wajen tsaron kasarmu da zaman lafiya na duk duniya, kuma ana iya dogara da ita."

Yau, galibin jama'ar kasar Sin sun kalli wannan bikin duba faretin soja ne ta gidajen talibijin da kuma sauraro rediyo da kuma shafin intanet. Mr. Li Deyu, wani mazauni birnin Beijing wanda ya kalli bikin a wani kanti ya ce, "Wannan biki yana da kyau. Ya karfafa gwiwarmu. Idan kasar ta samu karfi, jama'a za su iya samun arziki. Ka ga, dukkansu na'urori da makamai ne na zamani."

A cikin shekaru 10 na farko bayan kafuwar sabuwar kasar Sin, a ko wace shekara, kasar Sin kan yi bikin duba faretin soja. Amma a sakamakon dalilai da yawa a gida, ba ta ci gaba da yin irin wannan biki ba har sai bayan da ta fara yin gyare-gyare a gida da kuma bude kofa ga waje a shekarar 1978. A shekarar 1984 da ta 1999, Sin ta yi bikin duba faretin soja sau 2.

A cikin shekaru 10 da suka wuce, kasar Sin ta fi samun saurin bunkasuwa. Haka kuma, wadannan shekaru 10 na da matukar muhimmanci gare ta wajen yin gyare-gyare kan rundunar sojanta. Ta haka, bikin duba faretin soja da aka yi a bana ya fi jawo hankali sosai. Manjo-janar Luo Yuan da ya fito daga kwalejin nazarin kimiyyar aikin soja ta kasar Sin yana ganin cewa, yawan sojojin da suka shiga bikin da kuma yawan na'urori da kayayyakin soja da aka nuna a bikin sun nuna cewa, rundunar sojan Sin ta samu babban ci gaba ta fuskar zamanintar da kanta a fannoni 2. Manjo-janar Luo ya ce, "A maimakon mai da hankali kan yawan sojoji kawai, yanzu Sin na dora muhimmanci kan ingancin sojoji da kuma fasahohinsu. Ta kara sanya kimiyya da fassaha ta zamani cikin harkokin sojojinta. Sa'an nan kuma, ta kyautata na'urori da kayayyakin soja matuka daga fannoni 2, wato ta hanyar aikin sadarwa da kuma daukar matakan soja cikin hadin gwiwa."

Kana kuma, a ganin manjo-janar Luo, kasar Sin ta yi bikin duba faretin soja ne ba domin nuna karfinta na soja ba. An danka wa sojojin kasar Sin nauyin kiyaye ikon mulkin kasa da tsaron kasa da cikakken yankin kasa gami da kiyaye zaman lafiya a duk duniya gaba daya. manjo-janar Luo ya ce, "Kasarmu ta yi bikin duba faretin soja ne domin bayyana wa kasashen duniya da jama'ar Sin burinta da kwarewarta a harkokin aikin soja ba tare da boye kome ba."

1 2