Bisa matsayinsa na daya daga cikin manyan dakunan wasannin motsa jiki na Olympics, dakin wasan ninkaya na 'water cubic' ya janyo hankalin masu yawon shakatawa na gida da na waje. Sai dai mafi yawan mazauna birnin Beijing sun fi so su motsa jiki a dakunan wadanda ba su yi nisa da gidajensu. Li Zhaoqian, da ke da shekaru 32 da haihuwa, wani ma'aikacin kamfani ne, ya kan buga kwallon raga tare da abokansa. Amma, da ya zo dakin wasan kwallon raga na Olympics da ke cikin jami'ar fasaha ta Beijing, abin da ya gani ya burge shi sosai.
'Dakin babu almubazzaranci a ciki. Ina tsammanin an fi mai da hankali kan saukin amfani da shi.'
Don share fagen wasannin Olympics, gwamnatin birnin Beijing ta gina dakunan wasannin Olympics da yawa, haka kuma, ta ware makudan kudade da ba a taba ganin irinsu a da ba wajen inganta kayan more rayuwa. Sa'an nan rabin yawan wadannan kudade aka yi amfani da su don gina layin dogo, da hanyar mota, da filin jirgin sama, da dai sauransu. Ta hakan, an samar da wani yanar zirga-zirga mai sauri a cikin birnin. Abin ya sa mazauna birnin suka samu sauki lokacin da suka fita waje. Kamar dai yadda Madam Bi Ziyu take, da ma, ta kan sauya motocin bos har sau 2 don tafiya zuwa wurin aiki. Ko dai ta tuka motar kanta, ta kan gamu da cunkuson motoci a kan hanya. Shi ne ya kan sa ta yi awoyi 2 a hanya a ko wace safiya. Amma yanzu, wasu sabbin jiragen kasa da ke gudu a karkashin kasa sun hada gidanta da wurin aikinta, hakan ya sa ta samu sauki sosai.
'Domin share fagen taron wasannin Olympics, an shimfida sabon layin dogo don jirgin kasa da ke gudu a karkashin kasa. Akwai wani layin 5 da ya tashi daga gidana, shi ya sa zan iya shiga jirgi na layin 5, daga baya na sauya zuwa layin 10, wanda zai kai ni wajen ofis. Hakan ya ba ni sauki, ya sa na bar wahala ta da . Duk inda na je, akwai jirgin kasa da zai ba ni taimako.'
A lokacin da aka shirya wasannin Olympics a birnin Beijing a shekarar 2008, gwamnatin birnin ta fara aiwatar da matakin hana fitowar motoci bisa lambobinsu na mara ko na cika. Abun ya saukaka cunkuson da aka samu a kan hanya, haka kuma ya kyautata yanayin birnin. Bisa matakin, masu motoci sun yi hakuri, sun samarwa birnin Beijing da wani muhalli mai kyau. Shi ya sa ana ci gaba da aiwatar da matakin hana fitowar motoci bisa lambobinsu, wanda ya samu goyon baya daga mafi yawan mazauna birnin Beijing. Madam Bi Ziyu ta ce,
'Ana ta kara samun motoci a birnin Beijing. Matakin da aka dauka na hana fitowar motoci zai iya saukaka matsin lambar da aka samu kan aikin zirga-zirga. An rage yawan motocin da ke gudu kan hanya, ta hakan an rage yawan iskar guba da motocin suka fitar. Shi ya sa yanzu ba na tuka mota a ko wace ranar aiki, don tabbatar da saukin tafiya, da kuma rage yawan kudin da na kashe. Sai dai a karshen mako, ina tuka mota, hakan ya fi tsimin kudi, kuma zai amfanawa aikin kiyaye muhalli.'
A wajen taron wasannin Olympic da aka yi a birnin Beijing a shekarar 2008, masu aikin sa kai dubu daruruwa sun ba da taimako wajen shirya taron wasannin, inda suka nuna wa mutanen duniya zafin nama da son baki na jama'ar kasar Sin. Sai dai bayan taron Olympics, har zuwa yanzu, wasunsu na ci gaba da samar da hidima ga jama'a. Ji Peng, wanda ke da shekaru 19 da haihuwa, ya kasance daya daga cikin wadannan mutane. Ya taba aikin a cikin filin shakatawa na wasannin Olympics, inda ya amsa wa manema labaru, da 'yan wasan kasashe daban daban tambayoyinsu. Bayan Olympics kuma, ya zama wani mai kula da aikin sa kai na birnin Beijing, ya kan samar da taimako ga mutanen da ke yawon shakatawa a dakin wasan ninkaya na 'water cubic'. (Bello Wang) 1 2
|