Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-09 16:17:08    
'Yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasar Sin sun samu karifn zuciya a Berlin

cri

Kamar yadda Mr. Feng ya fada, 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle sabbin jini sun fitar da kansu daga matsin lamba, sun yi karawa da saura cikin sakin jiki. Abubuwan da Bai Xue ta yi, kayan shaida ne a wannan fanni. A yayin da aka rage sauran kilomita 1.195 da kammala gudun Marathon, Bai Xue ta cire hular da ta sanya a kai, ta jefa ta a wani gefe, daga baya, ta taka babban taki zuwa gaba. Cikin gajeren lokaci ta tsawaita zango a tsakaninta da Yoshimi Ozaki, abokiyar karawarta, 'yar kasar Japan. Ta kuma wuce ta layin karshe bisa babban fifiko. Jefa hularta a lokacin gudu ya nuna wa saura karfin zuciya da aniyar Bai Xue ta samun wannan lambar zinariya. A yayin da ta waiwayi abubuwan da suka faru a wancan lokaci, Bai Xue ta ce,"A wancan lokaci, na kasance cikin hali mai kyau. A cikin rukuni na farko, ya rage sauran 'yan wasa 3 ne kawai. A karo na farko ne na shiga irin wannan muhimmiyar gasar kasa da kasa, ta haka a ganina, na taki sa'a idan na sami lambar yabo. Amma bayan da na jefa hulata, na yi aniyar zama zakara. Shi ya sa na rubanya kokarina, har na wuce ta layin karshe."

Ko ya dake ba zai yiwu ba ko wane dan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasar Sin da ya shiga gasar a Berlin ya gaza samun lambar zinariya ko ta azrufa, amma sun yi kokarinsu domin samun maki mai kyau. 'Yar wasan Hammer Zhang Wenxiu ta kasar Sin ta zama ta 5 kawai a wannan karo, amma ba ta rasa karfin zuciyarta ba. A maimakon rasa karfin zuciya, ba tare da duban bakin gatari ba ta bayyana cewa, ba za ta canza nufinta na zama zakara a duk duniya ba. Tana mai cewar,"Ko da yake ban yi abubuwa yadda ya kamata a cikin gasar ba, amma ba zan canza nufina ba. Wadda ta zama zakara ta karya matsayin bajinta na duniya bisa kwarewarta. Yana kasancewa gibi a tsakanina da ita, ko da yake idan na nuna karfina mafi kyau. Duk da haka, a ganina, ba zan iya umartar saura ba, sai ni kaina. Ina fatan zan kara inganta karfina cikin sauri. Babu tantama ina da karfin zuciya. Kuma ba zan canza nufina na zama zakara ta duk duniya ba."

Kamar yadda Zhang Wenxiu ta fada, bisa rubanya kokarinsu a birnin Berlin, dukkan 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasar Sin, wadanda karfinsu ya sha bamban, kuma makinsu ya sha bamban, sun nuna wa saura cewa, a birnin Berlin, kungiyar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Sin ta samu karfin zuciya da kuma kyakkyawan fata.(Tasallah)


1 2 3