Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-09-09 16:17:08    
'Yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasar Sin sun samu karifn zuciya a Berlin

cri

A yayin gasar wasannin Olympic ta Beijing da aka yi a shekarar bara, Bai Xue ta zama ta 21 a cikin wasan gudu mai tsawon mita dubu 10. Ba ita kawai ba, sauran 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle su ma ba su samu maki mai kyau ba, in an kwatanta su da sauran 'yan wasan kasar Sin. Ba tare da boye kome ba Feng Shuyong, babban malamin horas da wasanni na kungiyar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Sin ya bayyana cewa, kungiyar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Sin ta gamu da tsananin wahala, wadda ba ta taba gamuwa da ita a da ba. Amma mawuyancin hali da suke ciki bai sanya 'yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle na kasar Sin su rasa karfin zuciya ko kadan ba, kuma ba su daina kokarinsu ba. Mr. Feng ya ce,"A yayin gasar wasannin Olympic ta Beijing, kungiyarmu ta fi fuskantar mawuyacin hali. Amma ba mu rasa karfin zuciya ba. A ganina, wannan na da muhimmanci. Na taba fuskantar mabambantan mawuyancin hali sau da yawa. Duk da haka ba mu daina kokarinmu ba. Ina tsammanin cewa, idan mun kara gudanar da aikinmu ta hanyar da ta dace, za mu iya samun ci gaba a wasu gasanni. Haka kuma, idan mun gano abubuwan kasawa da matsaloli, mun fitar da dabaru, ba mu daina kokarinmu ba, to, 'yan wasanmu za su iya samun isasshen karfin yin karawa da takwarorinsu na kasashen waje a wasu gasanni."

Kafin gasar fid da gwani ta kasa da kasa da aka yi a wannan karo, kungiyar kasar Sin ta tashi zuwa Berlin tare da nuna kankan da kai. Rabinsu sabbin jini ne da suka shiga gasar fid da gwani ta duniya a karo na farko. Burinsu shi ne samun lambar yabo kawai. Amma bayan budewar gasar ba da dadewa ba, 'yan wasan kasar Sin sabbin jini sun ba mutane mamaki da farin ciki da yawa. Wang Hao ya samu lambar azurfa a cikin wasan iya tafiya da sauri na tsawon kilomita 20 na maza. Daga baya kuma, Liu Hong ta samu lambar tagulla a cikin wasan iya tafiya da sauri na tsawon kilomita 20 na mata. Kungiyar wasan guje-guje da tsalle-tsalle ta kasar Sin da sabbin jini suka samu rinjaye sun yi karawa da takwarorinsu na kasashen waje cikin kwanciyar hankali da karfin zuciya da kuma kyakkyawan tunani. Wannan shi ne muhimmin tabbaci a gare su wajen yin fintikau a Berlin. Game da wannan, Mr. Feng ya furta cewa,"A ganina, wadannan 'yan wasan namu sabbin jini sun fi takwarorinsu tsoffin hannu kyau ta fuskar tunani. Ba su fuskanci matsin lamba sosai ba. A da mun sha cewa, sabbin jini ba su shiga isassun gasanni ba. A hakika, shiga gasanni da yawa ya zama wajibi a gare su, amma a kyakkyawan tunani na fi nuna muhimmanci. Ba za mu iya cimma burinmu ba, idan 'yan wasa ba su iya nuna gwanintarsu yadda ya kamata ba. A cikin irin wannan hali ne 'yan wasanmu sabbin jini suka nuna karfin zuciya kan gwanintarsu, kuma sun yi namijin kokarinsu."

1 2 3