Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-13 16:07:09    
Zabiyar kasar Sin mai suna Song Song

cri

Bikin rera wakoki na Song Song ya burge mutanen Rasha sosai. Sabo da haka, bayan Song Song ta koma kasar Sin, kwalejin kide-kide na Gnesin ya gayyace ta da ta koma kasar Rasha don nuna wasan kwaikwayo na La Traviata. Song Song ta cimma mafarkin da ta rike da shi tun daga take wata yarinya, ta yi farin ciki sosai.

Dadin dadawa, abin da ba za ta manta da shi ba shi ne, shugaban kasar Sin Hu Jintao ya gana da ita a shekarar 2005. A wancan shekara, shugaba Hu Jintao ya je birnin Moscow don halartar bikin taya murnar cika shekaru 60 da cimma nasarar yakin kin fascist na duniya. Bayan da Song Song ta rera wakoki ga tsoffin sojojin Rasha, shugaba Hu ya nuna goyon bayanta wajen zaman jakadar tuntubar Sin da Rasha a fannin al'adu. Song Song ta waiwayi cewa, "Ban zan manta da lokacin da na yi musafaha da shugaba Hu ba, ya ce, na iya rera waka sosai, ya kamata, na yi kokarin koyon fasahar rera wakoki daga wajen kwararru a fannin wasan fasaha na kasar Rasha, yana fatan zan zama jakadar musanyar ra'ayi a fannin al'adu a tsakanin kasashen biyu."

Song Song ta yi bikin rera wakoki ita kadai a birnin Shanghai bayan ta dawo kasar Sin, inda ta rera wakokin kasar Rasha. Yanzu, Song Song tana ci gaba da koyar da ilmin rera wakoki a kwalejin wasannin kwaikwayo na Shanghai, kuma tana shirya yin wani bikin rera wakoki don taya muryar wannan shekarar harshen Rasha ta kasar Sin, kana za ta halarci gasar rera wakokin Rasha ta Sinawa da CRI ta kira.


1 2 3