Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-13 16:07:09    
Zabiyar kasar Sin mai suna Song Song

cri

A shekarar 2004, kasar Sin ta tura Song Song zuwa kasar Rasha don koyon ilmin rera waka. Amma a gabannin haka, Song Song ba ta san kide-kiden Rasha ko kadan ba. Ta ce, "Ban taba sauraron wasan kwaikwayo na Rasha ba, amma na san kide-kiden Rasha sun fi kyau a duniya. Na san Pytor Llyich Tchaikovsky da shahararrun wakoki da wasannin kwaikwayo, amma ban taba rera su ba."

Amma isowarta a kasar Rasha ke da wuya, sai ta fara nuna kaunarta ga wannan kasa. Yanzu, ta waiwayi cewa, "Kasar Rasha tana cikin kyakkyawan hali a fannin wasan fasaha. Ta nuna fifikonta a fannonin gine-gine da zane-zane da mutum-mutumi da rawar ballet da adabi da wasannin kwaikwayo da kuma sauransu, dukkansu sun nuna al'adu masu siffar gargajiya sosai. Ina da lukuta da yawa don jin dadinsu da kuma koyon wadannan ilmi. Idan kana son jin dadin kide-kide da wake-wake, ka iya sauraron bikin kide-kide da wake-wake a kowace rana da dare, ka iya jin dadin wake-waken da kwararru a fannin rera waka na duniya suka rera. Idan ina da lokaci, na kan je nunin zane-zane da kuma sauran nune-nune. Ba zan manta da shekarun da nake karatu a kasar Rasha ba."

A lokacin da Song Song ke karatu a kasar Rasha, ta je birnin Saint Petersburg don sauraron wasannin kwaikwayo a shahararren babban gidan nuna wasan kwaikwayo na Mariinsky. Song Song ta ce, ta samu ilmi da yawa a wancan lokaci. Ta ce, "Na sha wahala sosai a kasar Rasha, amma a sa'i daya, na samu ilmi da yawa, na samu babbar ci gaba a fannoni da yawa, ban da wannan kuma, na nuna sha'awa sosai ga al'adu da wasan fasaha na kasar Rasha."

A lokacin da take kusan gama karatu a Rasha, Song Song ta yi niyyar kira wani bikin rera waka ita kadai. Wannan ne karo na farko da dalibar Sin ke iya yin irin wannan bikin rera waka a shahararren kwalejin kide-kide na kasar Rasha. Song Song ta ce, "Na rera wakoki ga malaman kwalejin, na samu mastin lamba sosai, galibin wakokin da na rera wakokin Rasha ne, dole ne na rera wadannan wakoki ta harshen Rasha."

A gun bikin, Song Song ta rera shahararrun wakoki fiye da goma, ciki har da wakokin shahararrun masu tsara wakoki. Ba ma kawai, wannan biki ya samu maraba daga wajen mutanen Rasha ba, hatta ma kwararru a fannin rera wakoki na Rasha sun nuna yabo ga kokarin da matashiya zabiyar kasar Sin ta yi da kuma ra'ayin kaunar aikin da ta nuna.

1 2 3