Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-11 09:39:41    
Klaus Schlappner na da shaukin kasar Sin

cri

A yayin da Mr. Schlappner ya taimakawa kasar Sin wajen shirya hadaddiyar gasar wasan kwallon kafa ta kwararru, kungiyar wasan kwallon kafa ta maza ta kasar Sin da ke karkashin shugabancinsa ta samu wasu ci gaba. Amma a cikin gasar tace wadanda za su shiga gasar cin kofin duniya ta kasar Amurka ta shekarar 1994 daga nahiyar Asiya, kungiyar kasar Sin ta sha kaye. Dan haka, Mr. Schlappner ya sa aya ga aikinsa na babban malamin horas da wasanni na kungiyar kasar Sin. Ko da yake bai sami makin da ya iya gamsuwa a matsayin babban malamin horas da wasanni na kungiyar kasar Sin ba, amma a ganin Mr. Schlappner, bai sha kaye a kasar Sin a matsayin babban malamin horas da wasannin ba. Yana mai cewa,"Ba ni da isasshen lokaci. Abun bakin ciki shi ne a wancan lokaci ban iya taimakawa kungiyar kasar Sin ta shiga gasar cin kofin duniya ba. Duk da haka na kawo wa kungiyar kasar Sin sauye-sauye da yawa, kamar kula da 'yan wasa a tsanake domin sanyawa su dace da harkokin kwararru. Musamman ma na inganta aikin horaswa. 'Yan wasa da yawa daga cikin kungiyar kasar Sin a wancan lokaci, kamar Gao Hongbo da Fan Zhiyi, yanzu su ma sun zama malaman horas da wasanni. Sun riga sun aiwatar da ruhuna a matsayin malamin horas da wasanni a ayyukansu na yau da kullum. Hakan shi ne amincewar da aka nuna mini."

Bayan da ya bar kasar Sin, har kullum Mr. Schlappner yana mai da hankali kan wasan kwallon kafa na kasar Sin. Ya taba taimakawa 'yan wasan kasar Sin su je Jamus domin yin wasan kwallon kafa. Ya kuma yi amfani da kudinsa domin taimakawa malaman horas da wasanni na kasar Sin su je Jamus samun aikin horaswa. Bugu da kari kuma, ya himmantu wajen taimakawa kungiyar kasar Sin ta samari ko kuma yara su je Jamus domin kyautata karfinsu. Ya zuwa yanzu, Mr. Schlappner yana da hulda mai danko a tsakaninsa da wasan kwallon kafa na kasar Sin. E, haka ne, kamar abubuwan da ya fada, ya riga ya hada zuciyarsa da wasan kwallon kafa na kasar Sin tare.(Tasallah)


1 2 3