Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-08-11 09:39:41    
Klaus Schlappner na da shaukin kasar Sin

cri

A nan kasar Sin, Mr. Schlappner ya fi wani dan kasar Jamus na daban Franz Beckenbauer shahara, wanda aka mayar da shi tamkar sarkin wasan kwallon kafa. Dalilin da ya sa haka shi ne Mr. Schlappner ya taba zama babban malamin horas da wasanni na kungiyar kasar Sin. Amma muhimmin dalilin shi ne saboda shi malamin horas da wasanni ne na farko da ya fito daga kasashen waje, ya kuma taimakawa kasar Sin wajen raya wasan kwallon kafa bayan da ta bude kofa ga waje da kuma yin gyare-gyare a gida. Dangane da dalilin da ya sa ya himmantu wajen raya wasan kwallon kafa na kasar Sin, Mr. Schlappner ya ambaci sunayen shugabanni 2 na kasar Sin. Yana mai cewar,"Kafin na zo nan kasar Sin, na yaba da Mr. Zhou Enlai da kuma Mr. Deng Xiaoping. Ina girmama su sosai. A lokacin da nake da kuruciya, na taba sauraren wasu abubuwan da Mr. Zhou ya fada. Sun burge ni sosai. Sannu a hankali, na fara sha'awar kasar Sin. Ina son in yi abubuwa domin wannan kasa."

Domin sanya kasar Sin ta dace da harkokin kasa da kasa ta fuskar wasan kwallon kafa cikin sauri, da kuma cika burin kasar Sin na shiga gasar cin kofin duniya ta wasan kwallon kafa tun da wuri, hadaddiyar hukumar harkokin wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta yi shirin zaben babban malamin horas da wasanni na kungiyar kasar Sin daga ketare. Babu matsala Mr. Schlappner da ya taba kasancewa daya daga cikin malaman horas da wasanni 10 mafi fice na shekara-shekara a Jamus ya bullowa kasar Sin. Mr. Schlappner ya gaya wa wakilinmu cewa,"A watan Afrilu na shekarar 1992, kasar Sin ta gayyace ni in zama babban malamin horas da wasanni na kungiyar kasar Sin. A wancan lokaci na yi aikin malamin horas da wasanni a wani kulob a Jamus, kana kuma, ina tafiyar da kamfanina. Ko na yi watsi da wadannan ayyuka duka, na zo nan kasar Sin domin zama babban malamin horas da wasanni ko a'a, wannan ya caza kaina."

A sakamakon matukar kulawa da kuma sha'awar da ya nuna wa wasan kwallon kafa na kasar Sin, a karshe dai Mr. Schlappner ya zama babban malamin horas da wasanni na kungiyar maza ta kasar Sin. Sa'an nan kuma, ya rage albashinsa dan radin kansa saboda hadaddiyar hukumar harkokin wasan kwallon kafa ta kasar Sin ba ta da isasshen kudi. A watan Yuni na shekarar 1992, Mr. Schlappner da hadaddiyar hukumar harkokin wasan kwallon kafa ta kasar Sin sun daddale yarjejeniyar aiki, ta haka wannan dan kasar Jamus ya zama babban malamin horas da wasanni na farko na kungiyar maza ta kasar Sin, wanda ya fito daga ketare, bayan da kasar Sin ta bude kofarta ga waje da kuma yin gyare-gyare a gida. Bayan da ya hau kan wannan kujera, Mr. Schlappner ya gano cewa, harsashi maras inganci da kasar Sin ta aza a wasan kwallon kafa ya wuce tunaninsa sosai. A wancan lokaci, kasar Sin ba ta shirya ko wace hadaddiyar gasar wasan kwallon kafa ta kwararru ba, kuma ba ta da isassun filayen wasa na aikin horaswa da kuma na'urorin aikin horaswa. Abun da ya kara caza kansa shi ne 'yan wasan kasar Sin ba su da tunani kamar yadda 'yan wasa kwararru suke da shi. Mr. Schlappner ya waiwaya da cewa, a wancan lokaci ya gano cewa, 'yan wasa da yawa na kasar Sin ssuna shan taba, ba su iya yin barci yadda ya kamata cikin dare. Hakan ya bakanta ransa sosai. Saboda haka, ba tare da bata lokaci ba, ya shawarci hadaddiyar hukumar harkokin wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta sanya harkokin wasan kwallon kafa su dace da harkokin kwararru cikin sauri. Inda ya ce,"Tun bayan da na fara shugabantar kungiyar kasar Sin, na bukaci 'yan wasa su yi abubuwa kamar yadda 'yan wasa kwararru su kan yi a tsanake. Ban da wannan kuma, na bai wa hadaddiyar hukumar harkokin wasan kwallon kafa ta kasar Sin shawarwari da yawa dangane da tsarin gudanar da hadaddiyar gasa ta kwararru da na tafiyar da kungiyoyi da sauran ruhun zamani. Na kuma ba da taimako wajen horar da malaman horas da wasanni da su dace da harkokin kwararru da kuma horar da 'yan wasa samari da yara. A wancan lokaci, na taba yin mabambantan ayyuka da yawa. Na kan yi kwanaki a kalla 6 ina aiki a ko wane mako. Takena a wancan lokaci shi ne sai aiki kawai babu tsayawa."

1 2 3