Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-28 21:04:02    
Hadin-gwiwar al'ummomin kasar Sin a jami'ar koyon ilimin likitanci ta Xinjiang

cri

Dalibai Ma Liang da Yusufucan suna zaune ne a bene guda a cikin wani gini, ko da yake su ba na kabila guda ba ne, amma kullum su kan yi wasan kwallo tare, da yin mu'amala da cudanya sosai. Bayan abkuwar tashin hankali a ranar 5 ga watan Yuli, Ma Liang da Yusufucan suna kara baiwa juna kulawa, kuma dangantakarsu na kara inganta, inda suka bayyana cewa:"Dangantakar dake tsakaninmu ta yi kyau kwarai da gaske. Jami'armu ta yi kama da wani babban gida, dalibai na kabilu daban-daban kamar 'yan uwa ne na juna, su kan yi wasan kwallo tare, da shirya ayyuka iri-iri cikin hadin-gwiwa."

Yayin da wakilinmu ke hira da daliban jami'ar koyon ilimin likitanci ta Xinjiang, dalibi Yusufucan ya gayawa wakilinmu wani labari cewa, a shekarar bara, wata daliba 'yar kabilar Han mai suna Wang Yanna dake karatu a jihar Xinjiang, ta bada kyautar kodarta ga wani dalibin makarantar midil dan kabilar Uyghur mai suna Maulacan wanda ya kamu da ciwo, kuma an yi wannan tiyata ne a wani asibiti dake cikin jami'ar koyon ilimin likitanci ta Xinjiang. Wannan lamari ya burge 'yan kabilu daban-daban a jihar. Yusufucan ya ce: "Wang Yanna ta bada kyautar kodarta ga Maulacan, wani dan karamar kabila. Maulacan dan kabilar Uyghur ne, Wang Yanna ita ce 'yar kabilar Han, wadda ta bada kyautar kodarta ga Maulacan ba tare da son-kai ba. Wannan lamari ya burge kowa da kowa."

1 2 3