"Ni ne wakilin jaridar Zaobao ta kasar Singapore, kasancewarta jam'iyyar da ke jan ragamar mulkin kasar da ta fi yawan mutane a duniya, shin ta wace hanya ce jam'iyyar kwaminis ta Sin ke sauraron ra'ayoyin jama'a?"
A ran 30 ga watan Yuni, a gun taron ofishin watsa labarai na majalisar gudanarwa ta Sin, wani dan jarida ya yi wa Mr.Li Zhongjie, mataimakin shugaban ofishin nazarin tarihin jam'iyyar kwaminis ta Sin wannan tambaya, kuma Mr.Li Zhongjie ya amsa da cewa,"kullum jam'iyyar kwaminis ta Sin na kokarin bayyana ra'ayoyin jama'a a cikin manufofinta. Sin na da halinta na musamman, sabo da haka, ya kamata mu bayyana ra'ayoyin jama'a bisa halin da kasar ke ciki, wato mu bi hanyar da ta fi dacewa wajen bayyana ra'ayoyin jama'a."
Mr.Li Zhongjie ya ba da karin haske da cewa, idan mun yi bayani a kan dimokuradiyya ta fannin ilmin siyasa, ma'anarta ita ce bisa doka ko kuma ka'ida a tsai da kuduri bisa ra'ayoyin akasarin jama'a. Har kullum jam'iyyar kwaminis ta Sin na tunani a kan ta wace hanya za a bayyana ra'ayoyin jama'a, ta kuma yi namijin kokari. Ya ce,"Jam'iyyar kwaminis ta Sin na kokarin bunkasa tafarkin dimokuradiyya a cikinta, kuma tana kokarin bayyana ra'ayoyin dukkan 'yan jam'iyyar a cikin manufofinta. Ban da wannan, a wajen kulawa da dangantakar da ke tsakanin jam'iyyar da jama'a, jam'iyyar na kokarin tuntubar jama'a da sauraron ra'ayoyinsu ta hanyar tarurrukan wakilan jam'iyyar da taron ba da shawarawari kan harkokin siyasa."
1 2 3
|