Gao Hongbo ya kan yi abubuwa ne kamar yadda ya fada. Ya taba yin amfani da kudinsa domin kyautata ilminsa a kasashen Jamus da Birtaniya da sauran kasashen da suka yi fice a wasan kwallon kafa. Ana bukatar raya wasan kwallon kafa na kasar Sin tare da yin koyi da fasahohin wadannan kasashe. A ganin Gao Hongbo, gwanancewa wajen yin koyi, fifiko ne mafi girma da yake nunawa a lokacin da yake matsayin malamin horas da wasanni. Yana mai cewar,"A halin yanzu, ilmi ya samu bunkasuwa da sauye-sauye cikin sauri, musamman ma gogayya a filin wasa. Akwai ka'idoji da yawa da suke samar mana nasara, shi ya sa muke bukatar kara sanin tunanin kasa da kasa ta fuskar wasan kwallon kafa a ko yaushe, daga baya kuma, za mu hada shi da halin musamman na kasarmu."
Wasu na damun makomar kungiyar kasar Sin da ke karkashin shugabancin Gao Hongbo. Dalilin da ya sa haka shi ne a matsayin malamin horas da wasanni, ya taba samun sabani tare da 'yan wasan kungiyarsa a sakamakon nuna taurin kai. Wani dan wasan kwallon kafa ya iya bin tsarin kansa wajen yin wasa da kwallon kafa, amma a matsayin babban malamin horas da wasanni, tilas ne a daidaita dangantaka a tsakanin bangarori daban daban yadda ya kamata. Bayan da ya zama babban malamin horas da wasanni na kungiyar kasar Sin, sannu a hankali, Gao Hongbo ya canza hanyar da ya saba bi a fannin yin mu'amala da tuntubar sauran mutane. Yana fatan abubuwan da ya faru a kansu a da, wadanda kuma ya haddasa sabani da yawa za su iya zama dukiya a gare shi wajen kasancewa malamin horas da wasanni a nan gaba. Inda ya ce,"A fannin horar da malamin horas da wasanni a fannin ilmi, yadda za a daidaita dangantaka a tsakaninsa da sauransu na da muhimmanci matuka a gare shi. A da, na taba daidaita dangantaka a tsakanina da sauransu yadda ya kamata, amma ina bukatar takaita abubuwan kasawa da na samu a wasu fannoni."
A shekarar da ta gabata, kasar Sin ta sha gamuwa da karantsaye a wasan kwallon kafa. A sakamakon kayen da kungiyoyin wasan kwallon kafa na kasar Sin masu mabambantan adadin shekaru da haihuwa suka sha, masu sha'awar wasan kwallon kafa na kasar Sin suna zura ido kan bullowar sabon jini da zai iya jagorantar kungiyar wasan kwallon kafa ta maza ta kasar Sin ta fita daga mawuyancin hali. Game da wannan, Gao Hongbo ya san wahala da matsin lambar da yake fuskanta sosai, duk da haka, ya nuna karfin zuciya sosai, yana kokarin jure wahalhalun da yake gamuwa. Ya bayyana cewa,"A zahiri, a matsayin wani malamin horas da wasanni, yanzu ina fuskantar matsaloli da dama. Amma tun da na zabi wannan aiki, to, tabbas ne zan fuskanci matsala. Za mu yi dabara, za mu zabi 'yan wasa mafi kyau, da fitar da dabarori mafi dacewa domin bude wa kasar Sin sabon shafi na raya wasan kwallon kafa."
Wannan shi ne Gao Hongbo, babban malamin horas da wasanni mafi kuruciya a tarihin kungiyar wasan kwallon kafa ta maza ta kasar Sin. Mai yiwuwa ne zai samar mana karin sabbin almara.(Tasallah) 1 2 3
|