Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-07-01 10:50:19    
Gao Hongbo, sabon malamin horas da wasanni na kungiyar wasan kwallon kafa ta maza ta kasar Sin

cri

Gao Hongbo, an haife shi ne a birnin Beijing, hedkwatar kasar Sin a shekarar 1966. Ya shiga kungiyar wasan kwallon kafa ta maza ta kasar Sin a shekarar 1989. Sa'an nan kuma, a shekarar 1999 ya yi ritaya a matsayin dan wasan kwallon kafa, amma a daidai wannan shekara ya zama malamin horas da wasanni. A shekarar 2007, a karkashin shugabancinsa ne kungiyar birnin Changchun ta zama zakara a cikin hadaddiyar gasar wasan kwallon kafa ta kasar Sin.

A watan Afrilu na shekarar da muke ciki, hadaddiyar kungiyar wasan kwallon kafa ta kasar Sin ta nada Gao Hongbo a matsayin babban malamin horas da wasanni na kungiyar wasan kwallon kafa ta maza ta kasar Sin. A ganin wasu, har kullum Gao Hongbo yana kasancewa cikin natsuwa. Haka kuma, sabanin da ke tsakaninsa da 'yan wasan kungiyarsa a lokacin da yake matsayin malamin horas da wasanni ya sanya wannan babban malamin horas da wasanni mafi kuruciya a tarihin kungiyar kasar Sin ya hadu da kalubale sosai tun daga farkon lokacin hawa kan kujerar babban malamin horas da wasanni na kungiyar kasar Sin. Amma bayan da wakilinmu ya zanta da Gao Hongbo, ya san karin abubuwa dangane da wannan sabon babban malamin horas da wasanni na kungiyar kasar Sin.

A lokacin da yake kasancewa dan wasa, Gao Hongbo ya gwanance ne sosai wajen jefa kwallon cikin raga, amma ya kan yi shiru, bai cika surutai da yawa ba. Wakilinmu ya fara zantawa da wannan babban malamin horas da wasanni mafi kuruciya na kungiyar wasan kwallon kafa ta maza ta kasar Sin ne game da halayyarsa. Amma kafin su fara hira, Gao Hongbo ya gyara bayanin da wakilinmu ya yi. Shi ba wani mutumin da ya kan rufe zuciya ga kowa ba ne, inda ya ce,"Da farko dai, ina so in gyara kuskuren da aka yi game da halayyata. A zahiri, ina son samun sabbin abokai matuka, ban taba rufe zuciyata ga kowa ba."

1 2 3