Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-30 23:06:02    
Zagayawa a farfajiyar da za a yi taron baje-koli na kasa da kasa a shekarar 2010 a birnin Shanghai

cri

Ji Lude, shugaban sashen bayyana babban take na hukumar kula da harkokin taron baje-koli na duniya na Shanghai ya fayyace cewa, za a nuna wani fim a dakin nune-nunen kasar Sin. Yana mai cewar,"Fim din zai bayyana mana kalubalen da aikin raya birane yake kawo wa kasar Sin a halin yanzu da kuma yadda kasar Sin take tinkarar wannan kalubale. Sa'an nan kuma, za mu kebe wani babban fili, inda za mu shirya harkokin nishadi da kuma sayar da abubuwa domin ba wa mutane damar kara fahimta kan abubuwan da za su faru a nan gaba."

A matsayinsa na muhimmin ginin da ya ratsa farfajiyar taron baje-koli na duniya na Shanghai a tsakiya, inda kuma mutane ke yin zirga-zirga, babban ginin Expo Axis mai benaye 2 bisa kasa da sauran 2 a karkashin kasa zai samar da hidima ta fuskar kasuwanci da abinci da nishadi da tarurukan nune-nune da kuma zirga-zirga.

1 2 3