Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2009-06-30 23:06:02    
Zagayawa a farfajiyar da za a yi taron baje-koli na kasa da kasa a shekarar 2010 a birnin Shanghai

cri

Mai yiwuwa ne kuna sane da cewa, za a yi taron baje-koli na kasa da kasa a birnin Shanghai na kasar Sin a shekarar 2010, wanda aka shisshirya irinsa sau 124 a mabambantan kasashe kusan 30 tun daga shekarar 1851. Babban takensa a wannan karo shi ne "kyautata birni domin ingantuwar zaman rayuwa". Mutane da yawa suna zura ido kan wannan kasaitaccen taro. To, mene ne za mu iya gani a birnin Shanghai? Yau ma za mu je birnin Shanghai tare domin yin yawo a farfajiyar taron baje-koli na kasa da kasa da ake ginawa, inda muke sa ran sheda yin wannan gagarumin taro a nan gaba.

Farfajiyar taron baje-koli na kasa da kasa na Shanghai na cikin yankin cibiyar Shanghai na kudu daidai, tana kasancewa a tsakanin muhimman gadoji 2 wato Lupu da Nanpu, sa'an nan kuma, kogin Huangpujiang da ya fi muhimmanci ga birnin Shanghai ya ratsa ta. Fadinta ya kai murabba'in kilomita 5.28, inda za a gina dukkan dakunan nune-nune da kauyen taron baje-koli na duniya da sauran gine-ginen da abin ya shafa. Diao Feicui, wata ma'aikaciyar hukumar kula da harkokin taron baje-koli na duniya na Shanghai, wadda ke kula da yayata taron ta yi karin bayani da cewa,"An raba dakunan nune-nune zuwa bangarori 5 bisa amfaninsu, wato bangare na A da B da C da D da kuma E. Dukkan dakunan nune-nune na kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa suna kasancewa yankin gabashin kogin Huangpujiang a cikin bangarori na A da B da kuma C. A yankin yammacin kogin Huangpujiang, mun yi kwaskwarima kan tsohon wuri na masana'antar kera jiragen ruwa ta Jiangnan domin samun bangare na D, inda masana'antu za su gina dakunan nune-nunensu. Haka kuma, bangaren E, sabon abu ne da za a samu a yayin taron baje-koli na kasa da kasa na Shanghai, inda bisa babban taken taron, za mu nuna batutuwan gina birane mafi dacewa da za a zaba a duk fadin duniya. Wannan bangare zai zama daya daga cikin abubuwan da suka jawo hankalin mutane."

Masu sauraro, in kun halarci taron baje-koil na duniya na Shanghai, da farko dai za ku san babban ginin da ke ratsa farfajiyar taron baje-koli na duniya wato Expo Axis, inda kuma yawancin hada-hada ke gudana, da kuma manyan dakunan nune-nune 4, wato dakin nune-nunen babban taken taron da na kasar Sin da cibiyar taron baje-koli na duniya da kuma cibiyar nuna wasanni. Su ne gine-ginen din din din da ake ginawa domin taron baje-koli na duniya na Shanghai. Yanzu bari mu gabatar muku da dakin nune-nunen kasar Sin. Surar wannan jan dakin nune-nune ta yi kama da hasumiyar Eiffel a kife. She Zhipeng, wani jami'in kula da ayyukan gine-gine na hukumar kula da harkokin taron baje-koli na duniya na Shanghai ya yi karin bayani da cewa, a cikin dakin nune-nunen kasar Sin, za a bayyana wa 'yan kallo fahimtar Sinawa kan babban taken taron, wato "Kyautata birni domin ingantuwar zaman rayuwa". Yana mai cewar,"Dakin nune-nunen kasar Sin zai bayyana wa mutane babban taken taron, wato 'Kyautata birni domin ingantuwar zaman rayuwa', inda mu Sinawa za mu yi karin bayani kan fahimtarmu dangane da wannan babban take, da yadda za mu aiwatar da shi da kuma zurfafa shi."

1 2 3